Cika shekaru 77: Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Cika shekaru 77: Gwamnonin Arewa sun taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Kafatanin gwamnonin yankin nahiyar Arewacin Najeriya sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da cika shekaru 77 a duniya a ranar Talata, 17 ga watan Disamba.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar inda ya jinjina ma Buhari bisa halinsa na dattaku, rikon amana, kishin kasa da kyakkyawan salon mulki.

KU KARANTA: Hotunan wasu mawaka da hadimin gwamnan Kebbi ya sa aka lakada musu dan banzan duka

“Salon mulkin Buhari ya kawo sauye sauyen masu kyau ta hanyar farfado da komadar tattalin arzikin kasa, kamfanoni da masana’antu, layukan dogo, noma da ma sauran sassa daban daban, wanda hakan ya tabbatar ma yan Najeriya cewa da gaske kake wajen ganin cigaban kasa.” Inji gwamnan.

Gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa, Dakta Simon Macham ya bayyana cewa tabbas Najeriya za ta samu cigaba mai daurewa daga irin salon mulkin shugaba Buhari na adalci, gaskiya da baje komai a faifai ga yan kasa.

Kungiyar gwamnonin ta kara da cewa yaki da rashawa da gwamnatin Buhari take yi ya kara martabar Najeriya a idon kasashen duniya, haka zalika yasa kasashen duniya suna girmama kasar.

Bugu da kari kungiyar gwamnonin ta jaddada biyayyarta ga shugaban kasa Buhari tare da burinta na bashi dukkanin goyon bayan da yake bukata wajen samun nasara ga ciyar da Najeriya gaba.

Daga karshe gwamnonin sun yi addu’ar Allah Ya kara ma shugaba Buhari lafiya, tsawon rai, basira, hikima, fikira da kuma kariyan Ubangiji amin.

A wani labari kuma, majalisar dokokin Najeriya ta kasafta naira biliyan 37 a cikin kasafin kudin shekarar 2020 na babban birnin tarayya Abuja domin yi ma majalisun biyu kwaskwarima da gyaran fuska.

Bugu da kari majalisar ta ware naira biliyan 100 domin ayyukan mazabu da kuma naira biliyan 1 don gudanar da gyare gyare a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel