Daga karshe: Fashola ya yi magana a kan damfarar da aka yi masa a yanar gizo

Daga karshe: Fashola ya yi magana a kan damfarar da aka yi masa a yanar gizo

Ministan aiyuka da gidaje ya yi karin bayani a kan rahoton kafafen yada labarai da ke ta yawo, na yadda wani dan damfarar yanar gizo ya damfaresa naira miliyan 3.1. A halin yanzu dan damfarar na hannun hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Babatunde Fashola, wanda ya sanar da cewa babu wani kasuwanci da ya auku tsakaninsa da wanda ake zargin har da zai sa ya damfareshi. Wannan kudin da ya samu sun kasance na aiyukan damfarar da yake yi a yanar gizon wanda ya samu a katin ministan na tafiye-tafiye.

A takardar da mai magana da yawun ministan, Hakeem Bello ya fitar, ministan ya ce, “Ganin yadda wanda ake zargin ya saba kutse cikin asusun bankin mutane na shekaru shida, ministan ya bibiyi lamarin wanda ake zargin har zuwa lokacin da aka samu shaidu gamsassu, sannan aka mika ga jami’an tsaro.”

DUBA WANNAN: Khadimul Islam: Ganduje ya sanya wa sabuwar gadar sama sunan wani babban malamin Islama

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta cafke Malik Wakili a kan zarginsa da ake da damfarar Fashola ta yanar gizo.

Mutumin mai matsakaicin shekaru, an zargesa ne da amfani da sunan Fashola wajen satar N3,106,216. Ya gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya ta jihar Legas, yankin Kudu maso Yamma a kasar Najeriya.

An zargi Wakili da hada kai da wani Abdullahi Umar, wajen amfani da sunan ministan don cimma wata manufa. Wannan laifin kuwa ya ci karo da sashi na 15 sakin layi na 2 da sashi na 27 sakin layi na 1, na dokokin hani da almundahanar kudade.

Ya musanta aikata laifuka ukun da ake zarginsa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel