Yan majalisa sun ware naira biliyan 37 domin gyaran majalisar dokokin Najeriya

Yan majalisa sun ware naira biliyan 37 domin gyaran majalisar dokokin Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya ta kasafta naira biliyan 37 a cikin kasafin kudin shekarar 2020 na babban birnin tarayya Abuja domin yi ma majalisun biyu kwaskwarima da gyaran fuska, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Bugu da kari majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta ware naira biliyan 100 domin ayyukan mazabu da kuma naira biliyan 1 don gudanar da gyare gyare a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

KU KARANTA: Har yanzu da sauran aiki kan batun kawar da talauci a Najeriya – Osinbajo

Duka wadannan kudade da ayyukan an sanyasu ne a cikin kasafin kudin babban birnin tarayya Abuja na shekarar 2020 wanda ya tasanma naira Tiriliyan 2.5. Da yake kare kasafin bukatunsu, shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa akwai bukatar canza abubuwa da dama a majalisar saboda sun tsufa sun tsofe.

“Kashi na farko na gyare gyaren zai fara ne da zauren majalisun biyu da dakunan kwamitocin majalisu, mun nemi N37bn, kuma an bayar, sai dai ba’a a hannun majalisa aka sanya su ba, suna hannun hukumar babban birnin tarayya Abuja ne, abinda muke so kawai shi ne a gyara majalisar.” Inji shi.

Sai dai daraktan watsa labaru na majalisar, Rawlings Agada ya bayyana shakkunsa game da isar kudaden, inda yake ganin ba lallai su isa wajen gudanar da wannan muhimmin aiki a majalisar ba.

“Akwai ayyuka da dama da ake bukata a majalisa, bana jin kudin nan zasu isa, saboda hatta hasumiyar majalisar na digar da ruwa, kuma akwai tsoron idan har ba’a gyara shi ba za’a iya fuskantar matsala a gaba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta kaddamar da bincike a kan wasu makudan kudade har naira biliyan 14.8 da suka yi batan dabo daga lalitar hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam.

Kwamitin majalisa mai kula da asusun gwamnati ne ya kaddamar da bincike biyo bayan korafi da mai binciken kudi na kasa yayi game da kudaden hukumar kwastam, inda yayi zargin akwai lauje cikin nadi game da binciken kudi da aka yi ma kwastam a tsakanin shekarun 2013 da 2014.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel