Har yanzu da sauran aiki kan batun kawar da talauci a Najeriya – Osinbajo

Har yanzu da sauran aiki kan batun kawar da talauci a Najeriya – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa sauran kasashen duniya sun yi ma Najeriya fintinkau wajen batun yaki da talauci tare da kawar da talauci a tsakanin al’ummominsu.

Jaridar The Cables ta ruwaito Osinbajo ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a bikin murnar cikar tsohon gwamnan jahar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi, shekaru 70 a rayuwa, inda yace Najeriya bata samu wani nasara wajen yaki da talauci ba saboda rashin takamaimen tsarin yin hakan daga gwamnatocin baya.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta dage dakatarwar da ta yi ma Rochas, da gwamnan jahar Ondo

“Tabbas an bar mu a baya wajen yaki da talauci, dalili kuwa shine kafin zuwan gwamnatinmu babu wani takaimaimen tsarin yin hakan, wannan shi ne dalilin da yasa daga shekarar 2014 zuwa 2015, APC ta sanya tsarin tallafi ga yan kasa a cikin manufofin jam’iyyar.

“Don haka da wannan tsarin tallafi ne zamu yi maganin talauci, tsari ne mai matukar muhimmanci, wanda babu irinsa a nahiyar Afirka, sai da bankin duniya ta yi nazari mai tsawo game da tsarin sa’annan ta amince ta zama abokiyar tafiyarmu a cikinsa.” Inji shi.

A nasa jawabi, tsohon gwamnan jahar Osun, kuma ministan al’amuran cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa idan har ana son kawar da talauci a Najeriya, sai an tatsi attajira ta hanyar haraji sosai da sosai.

“Haka zalika dole ne sai an tabbatar da gaskiya da adalci a tsare tsaren bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma yaki da rashawa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, majalisar wakilai ta kaddamar da bincike a kan wasu makudan kudade har naira biliyan 14.8 da suka yi batan dabo daga lalitar hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam.

Kwamitin majalisa mai kula da asusun gwamnati ne ya kaddamar da bincike biyo bayan korafi da mai binciken kudi na kasa yayi game da kudaden hukumar kwastam, inda yayi zargin akwai lauje cikin nadi game da binciken kudi da aka yi ma kwastam a tsakanin shekarun 2013 da 2014.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel