Majalisa ta fara binciken N14.8bn da suka yi batan dabo dsaga hukumar kwastam

Majalisa ta fara binciken N14.8bn da suka yi batan dabo dsaga hukumar kwastam

Majalisar wakilai ta kaddamar da bincike a kan wasu makudan kudade har naira biliyan 14.8 da suka yi batan dabo daga lalitar hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamitin majalisa mai kula da asusun gwamnati ne ya kaddamar da bincike biyo bayan korafi da mai binciken kudi na kasa yayi game da kudaden hukumar kwastam, inda yayi zargin akwai lauje cikin nadi game da binciken kudi da aka yi ma kwastam a tsakanin shekarun 2013 da 2014.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta dage dakatarwar da ta yi ma Rochas, da gwamnan jahar Ondo

Da yake bayar da jawabi a gaban kwamitin, shugaban hukumar kwastam, Hamid Ali ya bayyana cewa babu wani binciken asusun kudin hukumar kwastam da aka yi a tsawon shekaru domin kuwa hukumar kula da saye saye na gwamnati bata basu izinin yin hakan ba.

Ali, wanda ya samu wakilcin wani jami’I daga bangaren kudi na hukumar, S.I Ibrahim ya bayyana ma kwamitin cewa: “Ina so na shaida ma kwamitin nan cewa babu wani asusun hukumar nan da aka taba yi ma bincike domin kuwa BPP basu bamu izinin dauko hayar masu binciken kudi don aikin ba.

“Kafin fara amfani da tsarin asusun bai daya, TSA, bankuna 28 ne ke karbar kudade a madadin hukumar kwastam.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani mutumi daya shahara a wajen tafka mummunan dabi’ar damfara, Malik Wakili, da laifin damfarar minista kuma tsohon gwamnan jahar Legas.

EFCC ta tasa keyar Wakili gaban kotu ne bisa zarginsa da damfarar ministan ayyuka da gidaje a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola naira miliyan 3.1.

A ranar Litinin, 16 ga watan Disamba ne jami’an EFCC suka gurfanar da wannan gagararren dan damfara gaban babban kotun tarayya dake karkashin Alkali Mai Sharia Chukwujekwu Aneke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel