An jima Shugaba Buhari zai sa hannu a kundin kasafin kudin badi

An jima Shugaba Buhari zai sa hannu a kundin kasafin kudin badi

A yau Talata, 18 ga Watan Disamban 2019, ake sa ran cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai rattaba hannunsa a kan kasafin kudin shekara mai zuwa inji Jaridar nan ta Daily Trust.

A farkon makon nan aka samu rahoto cewa kundin kasafin kudin ya bar hannun majalisa ya zo fadar shugaban kasa. ‘Yan majalisar tarayya sun karkare duk aikin da za su yi a kan kundin.

A Ranar 8 ga Watan Oktoban 2019 ne shugaban kasa Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar na badi a gaban ‘Yan majalisa. Gwamnatin tarayya ta yi kasafin Naira tirilyan 10.33 ne a 2020.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasafin zai kara kokarin taimakawa wajen samar da aikin yi da bunkasa tattalin arziki. Wannan ne kasafin da ya fi kowane yawa da aka taba yi a Najeriya.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta fadawa Shugaba Buhari ya rika bin doka

An jima Shugaba Buhari zai sa hannu a kundin kasafin kudin badi
Kila an jima shugaba Buhari ya sa hannu a kasafin kudin shekara mai zuwa
Asali: Facebook

Majalisar Dattawa da ta Wakilan tarayya duk sun amince da kasafin kudin na shekara mai zuwa. Sai dai ‘Yan majalisar sun kara kudin da aka ware daga Naira Tiriliyan 10.33 zuwa Tiriliyan 10.63.

Majalisar tarayya ta kuma yi na’am da hasashen hako danyan mai da aka yi, sai dai ta kara kudin goron da aka yi wa farashin gangar man da shugaba Buhari ya yi, ganin yadda kasuwar mai ta ke.

Legit.ng ta fahimci cewa idan ta tabbata an sa hannu a kan wannan kundin kasafin kudi yau, ya zo daidai da ranar da shugaban kasar ya ke bikin murnar cika shekaru 77 da haihuwa a Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel