Dara ta ci gida: Oshiomole hatsabibin makaryaci ne - Gwamnan jihar Edo

Dara ta ci gida: Oshiomole hatsabibin makaryaci ne - Gwamnan jihar Edo

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya siffanta shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole a matsayin hatsabibin makaryaci wanda bai kamata arika sauraronsa ba.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Mista Crusoe Osagie.

Osagie ya bayyana hakan ne yayin martani kan jawabin Oshiomole da ya ce gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu basu da karfin siyasa a mazabunsu saboda hakan ya bayyana a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Oshiomole ya bayyana cewa saboda tsananin rashin karfinsu, dan jam'iyyar PDP ke wakiltar gwamnan a majalisar dattawan tarayya da kuma majalisar wakilai.

Amma a martanin gwamnan jihar, ya musanya ikirarin Oshiomole inda yace APC ta lashe kuri'un akwatinsa a zaben shugaban kasa kuma yafi samawa shugaba Buhari kuri'u fiye da Oshiomole.

Mai magana da yawun gwamnan jihar ya kara da cewa duk da abin kunyar da ya faru a gidan Oshiomole lokacin da akaci mutuncin sarkin Legas, Rilwan Akiolu; Oshiomole bai ji kunyar fitowa ya fadawa duniya cewa mataimakin gwamna, Philip Shaibu, ke da alhakin rikicin ba.

"Shugaban jam'iyyar ya ce kwamishana daya kadai ya nada a majalisar gwamna, wannan karya ne, ya zama mutane da dama domin suyi aiki da gwamnan wadanda suka hada da mataimakin gwamna, Shaibu, da sakataren gwamnatin jihar, Osarodion Ogie, da sauransu.

"A wani lokacin kuma, kwamishanan ya karyata Oshiomole a bainar jama'a lokacin da yayi ikirarin cewa an kai hari gidansa dake Benin. Kwamishanan ya karyata maganar kuma ya ce babu wanda ya kai hari gidan Oshiomole." A cewarsa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel