Yanzu-yanzu: Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 gobe

Yanzu-yanzu: Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 gobe

Muddin ba'a samu wani canji ba, shugaba Muhammadu Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 gobe Talata, 17 ga watan Disamba, 2019.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ranar 8 ga watan Oktoba, 2019 majalisar domin tabbatar da cewa na dawo zagayen Junairu zuwa Disamba na kowani shekara.

A ranar 13 ga watan Disamba, majalisar dokokin tarayya ta aikawa shugaba Muhammadu Buhari da kasafin kudin inda fadar shugaban kasa tace shugaba Buhari da majalisar zantarwa zasu zauna domin dubi cikin takardar.

A ranar 5 ga Disamba, 2019, Yan majalisan sun tabbatar da kasafin kudin ne bayan kimanin kwanaki arba'in da shugaban kasa ya gabatar da takardan gabansu.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Sanata Barau Jibrin, ya kawo kasafin majalisa bayan kwamitinsa ta kammala bincikenta.

Yan majalisun sun kara kudin da Buhari ya gabatar daga N10.33 trillion zuwa N10.6 trillion (10,594,362,364,830).

A jawabinsa, Barau Jibrin ya bayyana cewa bisa lissafin hakar gangan mai milyan 2.18 a rana, sun mayar da farashin kowani gangan zuwa $57 daga $55 da Buhari ya gabatar; sun kara $2.

KU DUBA NAN Yadda 'dan maina ya cire N58m daga bankin UBA - EFCC

Ga kiyasin da aka gina kasafin kudin kai da hotunan taron:

Danyen man da za'a rika haka a rana: Ganga milyan 2.18

Farashin kowani Ganga daya a : $57

Farashin Dala: N305 / $

Kudin shigan da ake sa ran samu a shekerar 2020:

Dagar arzikin Man fetur : 2.64 trillion

Arzikin Sabanin Mai (Haraji) : 1.81 trillion

Sauran hanyoyi ( sauransu) : 3.7 Trillion

Source: Legit

Tags:
Online view pixel