Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi (Hotuna)

Sama da mata 100 masu shekaru daga 50 zuwa 80 ne daga Agubia a karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi suka fito zanga-zanga tsirara. Sun yi hakan ne sakamakon cafke 'ya'yansu da jami'an tsaro a jihar suka yi.

Tsoffin matan sun garzaya gidan gwamnatin jihar ne wajen karfe 11 na safiyar ranar Litinin, da bukatar a gaggauta sakin 'ya'yansu wadanda jami'an tsaro suka kama sakamakon hargitsi da ya tashi a yankin cikin kwanakin nan.

Duk da manufar matan bata wuce ganin gwamnan jihar kai tsaye ba, amma jami'an tsaron gidan gwamnatin da ke Abakaliki sun haramta musu shiga.

Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi

Naked women protesting
Source: Facebook

Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi

Naked women protesting
Source: Facebook

An gano cewa, mummunan hargitsi ya auku a tsakanin kungiyoyi biyu kishiyoyin juna a jihar, a makonnin hudu da suka gabata. Kowacce kungiya na fafutukar ganin ta mallake tare da juya babbar tashar motar da ke yankin. Hakan kuwa ya jawo rashin rayuka da yawa a yankin inda wasu da yawa suka jigata. Hakazalika, kadarorin miliyoyin naira sun halaka.

Mercy Nwali, wacce ta yi magana da yawun matan, ta ce makasudin zanga-zangarsu bai wuce neman sasanci ba don kuwa rayukansu da na iyalansu na ciki hatsari.

DUBA WANNAN: Gwamnonin PDP biyu sun yi cacar baki a kan Buhari

"Abinda muke bukata shine su tsaya mu sasanta tsakaninmu. Ba zai yuwu suna birni ba amma suna tada hankulanmu da ke kauye. Ba ma bacci a gidajenmu kuma muna bukatar gwamnati ta saka baki," ta yi bayani.

Wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Juliana Nwali, ta sanar da jaridar Daily Trust cewa 'ya'yanta uku ne ke garkame a wajen jami'an tsaro.

A takaice dai, kokarin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Honarabul Stanley Okoro ne yasa matan suka bar kofar gidan gwamnatin.

Sama da mata 100 ne suka fito zanga-zanga tsirara a kan kama 'ya'yansu da jami'an tsaro suka yi

Naked women protesting
Source: Facebook

"Kun san cewa ku iyayenmu ne. Gwamnanmu bai yi farin cikin ganinku a wannan halin ba. Ina tabbatar muku da cewa, za a shawo kan matsalarku da gaggawa," in ji shi.

Ya bukacesu da su koma gida tare da tabbacin zaman lafiya zai dawo yankin din-din-din.

Amma kuma, matan sun ki karbar kudin mota ko shiga bas din da gwamnatin ta bada don mayar dasu Agubia.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel