Sowore: Sai mun yi wa doka biyayya – Shugaban Majalisa, Lawan

Sowore: Sai mun yi wa doka biyayya – Shugaban Majalisa, Lawan

Bayan korafe-korafe da suka daga jam’a da-dama, shugaban majalisar dattawan Najeriya. Ahmad Ibrahim Lawan, ya sa baki a game da takaddamar Yele Sowore da jami’an tsaro.

Sanata Ahmad Lawan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta zama mai bin dokar kasa. Jaridar Premium Times, ta rahoto cewa Sanatan ya yi wannan magana ne yau Litinin a Abuja.

Ahmad Lawan ya amsa tambayoyi ne daga bakin Manema labarai a Ranar 16 ga Watan Disamban 2019, game da yawan sabawa dokoki da tsarin mulki da wannan gwamnatin ta ke yi.

Sanatan Sanataocin ya ce dokar kasa abu ne da ya zama dole gwamnati ta bi. A cewarsa, daga cikin bin doka shi ne ganin an gurfanar da duk wani da ake zargi da laifi a gaban kotu.

KU KARANTA: An tsige wani Basaraken kasar Kano

Bayan haka kuma Mai girma Sanata Dr. Ahmad Lawan ya ce sakin wadanda ake kara bayan an same su ba da laifin da ake tuhumarsu ba a kotu, duk ya na cikin bin doka sau-da-kafa.

Sanatan na Arewacin jihar Yobe ya karasa jawabin na sa da cewa: “Idan ba a samu mutum da wani laifi ba, bai kamata a cigaba da wahalar da shi babu gaira babu dalili ba.”

An dade ana zargin gwamnati mai-ci da keta alfarmar Bayin Allah da yi wa dokar kasa karon tsaye. Yanzu haka ana cigaba da tsare Omoyele Sowore da wasu duk da an bada belinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel