INEC: Ba za mu iya sauya sunan Sanata Akpabio a takarar Majalisar Akwa-Ibom ba

INEC: Ba za mu iya sauya sunan Sanata Akpabio a takarar Majalisar Akwa-Ibom ba

Hukumar INEC mai zaman kanta, ta bayyana cewa jam’iyyar APC ba za ta samu damar sauya ‘dan takararta a zaben kujerar Sanatan Akwa Ibom da za a sake yi nan da ‘yan kwanaki ba.

INEC ta nuna cewa APC ba ta da hurumin canza wanda zai rike mata tuta a zaben Majalisar dattawa bayan Sanata Godswill Akpabio ya janye daga takara da Sanata mai-ci Chris Ekpenyong.

Sanata Godswill Akpabio ya nuna cewa bai da niyyar sake gwabzawa da Chris Ekpenyong wanda ya ke wakiltar Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar PDP, wanda a baya ya ke kalubalantar nasararsa.

Hakan na zuwa ne bayan Alkali ya bada umarni a sake gudanar da zabe a Yankin Essien Udim, a sakamakon karar da Godswill Akpabio ya shigar na cewa shi ne ya lashe zaben Sanatan yankin.

KU KARANTA: Wani mutumi ya damfari daya daga cikin Ministocin Shugaba Buhari

Bayan samun kujerar Ministan harkokin Neja-Delta a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, Ministan ya bukaci INEC ta nemo wani ‘Dan takarar da zai maye gurbinsa a karashen zaben.

Hukumar INEC mai gudanar da zabe, a wata hira da ta yi da ‘Yan jarida, ta yi karin haske game da lamarin, ta ke cewa duk wanda ya shiga takarar tun farko, zai sake ganin sunansa a yanzu.

Kwamishinan wayar da kan jama’a da yada labarai na INEC, Festus Okoye, ya bayyana cewa lokacin canza sunayen ‘yan takara ya wuce tun tuni, don haka jam’iyyar ta APC ta riga ta makara.

Okoye ya ce tun a Ranar 17 ga Wantan Nuwamban 2019, aka daina karbar canjin sunaye ko kuma ficewa daga takarar karashen zabukan da za a yi, kamar yadda sashe na 35 da dokar zabe ya ce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel