Za mu baiwa Buhari daman amso bashin $30m - Ahmad Lawan

Za mu baiwa Buhari daman amso bashin $30m - Ahmad Lawan

- Majalisar dattawa za ta baiwa Buhari daman karban bashin, a cewar shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan

- Buhari ya gabatar da bukatar bashin $29.96 billion ga majalisar dattawa

- Za ku tuna cewa shugaba Buhari ya gabatar da irin wannan bukatar lokacin Bukola Saraki amma suka hanashi

Daga karshe, shugaba Muhammadu Buhari zai samu biyan bukatarsa yayinda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa majalisar zata baiwa shugaban kasa daman karban bashin $29.96 billion.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai a Abuja.

A cewarsa, majalisar zata sa ido kan yadda za'a kashe kudin idan an karbo.

Lawan yace: "Zamu sanya ido yadda duk sisin da aka karbo sai an sa cikin wani aiki."

A ranar 28 ga Nuwamba, shugaban majalisar dattawa ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aikawa majalisar ne bukatar karbar bashi daga bankin duniya.

Za ku tuna cewa majalisar dattawa karkashin tsohon shugabanta, Bukola Saraki, ta hana Buhari karbo bashin a shekarar 2016.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel