An kama Janar mai ritaya bisa laifin safarar makamai

An kama Janar mai ritaya bisa laifin safarar makamai

- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Abiya ta sanar da cewa ta kama tsohon janar a rundunar soji bisa zarginsa da hannu a safarar makamai

- Ene Okon, kwamishinan 'yan sandan jihar Abia, ne ya sanar da hakan ranar Litinin yayin holin wasu masu laifi

- Rundunar soji ta gudanar da wasu sauye - sauyen wurin aiki da suka shafi manyan sojoji masu mukamin manjo janar guda 20 da birgediya janar 10

Rundunar 'yan sanda a jihar Abiya ta sanar da kama wani tsohon Janar a rundunar soji bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun makamai.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Abiya, Ene Okon, shine ya sanar da hakan yayin bajakolin wasu masu laifi a hedikwatar runduunar da ke Umuahia, babban birnin jiha.

Sai dai, Okon bai bayyana sunan tsohon janar din da rundunar 'yan sanda ta kama ba yayin da yake magana da manema labarai ba.

An kama Janar mai ritaya bisa laifin safarar makamai

'Yan sandan Najeriya
Source: Depositphotos

A wani labarin mai alaka da sojoji, rundunar soji ta gudanar da wasu sauye - sauyen wurin aiki da suka shafi manyan sojoji masu mukamin manjo janar guda 20.

DUBA WANNAN: Tsofin gwamnoni 6 na Arewa da kan iya fuskantar hukuncin da aka yanke wa Orji Kalu

Sauye - sauyen ya shafi manyan sojoji masu mukamin birgediya janar guda 10 yayin da rundunar sojin ta bayyana cewa ta yi sauyin wuraren aikin ne domin kara armashin aikin tsaron kasa da yaki da ta'addanci.

A cikin sanarwar da rundunar soji ta fitar a ranar Litinin, 16 ga watan Diamba, kakakinta na kasa, kanal Sagir Musa, ya bayyana cewa babban hafsan rundunar sojin kasa, laftanal janar Tukur Buratai, ya amince da sauye - sauyen da zasu fara aiki nan take.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel