Rai ba’a bakin komai ba: Miyagu sun banka ma wata Mata wuta a Abuja

Rai ba’a bakin komai ba: Miyagu sun banka ma wata Mata wuta a Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta kaddamar da bincike a kan yadda aka kashe wata Mata a Abuja ta hanyar banka mata wuta da ranta, inda ta kone kurmus.

Jaridar Premium Times ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan Abuja, Mariam Yusuf ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa data fitar, inda tace an tsinci kakkabin gawar matar ne a kan titin Area 3 yayin da Yansanda suke sintiri a karshen mako.

KU KARANTA: Toh fa! Malaman jami’ar OAU guda 3 sun mutu a cikin kwanaki 10

“Mun tsinci gawar mamaciyar ne a tattare a cikin jakar leda, amma babu wanda aka kama da hannu cikin kisan sakamakon muna cigaba da gudanar da bincike.” Inji Kaakaki Mariam Yusuf.

Da wannan ne Kaakaki Mariam ta bayyana cewa rundunar za ta dage damtse wajen tabbatar da tsaro a babban birnin tarayya Abuja domin kuwa akwai alamun miyagu sun kara huro wuta a Abuja yayin da bikin Kirismeti ke karatowa.

Daga karshe Kaakaki Mariam ta bayar da lambobin wayan rundunar Yansanda da jama’a zasu yi amfani dasu wajen kai rahoton duk wani mutumi da basu gane take takensa ba, ko wasu miyagun ayyuka kamar haka; 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883.

A wani labarin kuma, hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani mutumi daya shahara a wajen tafka mummunan dabi’ar damfara, Malik Wakili, da laifin damfarar minista kuma tsohon gwamnan jahar Legas.

EFCC ta tasa keyar Wakili gaban kotu ne bisa zarginsa da damfarar ministan ayyuka da gidaje a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola naira miliyan 3.1.

A ranar Litinin, 16 ga watan Disamba ne jami’an EFCC suka gurfanar da wannan gagararren dan damfara gaban babban kotun tarayya dake karkashin Alkali Mai Sharia Chukwujekwu Aneke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel