Naira miliyan 3.1: Minista Fashola fa fada hannun yan damfara

Naira miliyan 3.1: Minista Fashola fa fada hannun yan damfara

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani mutumi daya shahara a wajen tafka mummunan dabi’ar damfara, Malik Wakili, da laifin damfarar minista kuma tsohon gwamnan jahar Legas.

EFCC ta tasa keyar Wakili gaban kotu ne bisa zarginsa da damfarar ministan ayyuka da gidaje a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola naira miliyan 3.1, inji rahoton jaridar PM News.

KU KARANTA: Toh fa! Malaman jami’ar OAU guda 3 sun mutu a cikin kwanaki 10

A ranar Litinin, 16 ga watan Disamba ne jami’an EFCC suka gurfanar da wannan gagararren dan damfara gaban babban kotun tarayya dake karkashin Alkali Mai Sharia Chukwujekwu Aneke.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo sun kama wani jami’in rundunar Sojan Najeriya, Eyosu Kennedy mai shekau 25 da laifin tafka halin bera bayan ya saci wata mota kirar Toyota Camry.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’in Sojan mai mukam Private yana aiki ne a bataloya ta 112 dake jahar Borno, kuma an gabatar da shi ga yan jaridu ne a sakariyar Yansandan Najeriya dake garin Bini na jahar Edo.

Kwamishinan Yansandan jahar, Lawan Tanko Jimeta ya bayyana cewa Sojan ya sace motar ne daga babban birnin tarayya Abuja, inda ya kai ta jahar Edo domin ya sayar da ita, dubunsa ta cika ne a daidai lokacin da yake kokarin sayar da motar.

Haka zalika rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo ta samu nasarar cafke wasu gungun dakarun rundunar Sojin Najeriya dake da hannu cikin satar mutane, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Yansanda sun kama Sojojin ne tare da wani abokin aikinsu farar hula, inda suka tabbatar ma Yansanda cewa su ne suke fitinar jama’an garuruwan Agenebode, Fugar da sauran sassan jahar. Sojojin kamar haka; Collins Ameh, Balogun Taiwo da Evans Isibor.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel