An kori babban Malamin da ya so ya yi lalata da ‘Dalibarsa a Jami’ar Abuja

An kori babban Malamin da ya so ya yi lalata da ‘Dalibarsa a Jami’ar Abuja

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Jami’ar Tarayyar Najeriya da ke Abuja, ta sallami Shehin Malami kuma tsohon shugaban tsangayar koyar da harkar gona bisa zargin lalata da Mata.

Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin makarantar sun zauna sun game da zargin da ke kan wannan babban Malami na lalata da ‘Dalibai, a karshe su ka dauki matakin korarsa daga aiki.

Wani kwamiti na mutum-8 da aka kafa domin ya binciki Malamin makarantar shi ne ya bada wannan shawara wanda a karshe aka yi amfani da ita, aka kori Farfesan daga bakin aikinsa.

A tsakiyar wannan shekarar ne aka ji cewa Malamin ya bukaci wata ‘Dalibarsa ta ba shi hadin-kai ya yi lalata da ita domin ta samu damar cin jarrabawa. An saba yin irin wannan a jami’o’i.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya nemi Buhari ya bi a hankali da wasu Gwamnoni

Kafin nan dama jami’an ‘Yan Sanda sun taba yin ram da Malamin ya na kokarin tarawa da wata Baiwar Allah. Wannan bincike ya kai har gaban ofishin ‘Yan Sanda da ke Unguwar Gwarimpa.

Cafke Malamin da aka yi ya na yunkurin lalata ne ya sa wurin aikinsa su ka aika masa sammaci kwanaki. Kawo yanzu ba mu samu cikakken sunan wannan Malami da ya ke aikata alfasha ba.

Jaridar ta gano cewa Malamin da aka kora ya yi wa wata ‘Daliba mai lambar makaranta: 16211546, barazanar faduwa jarrabawarsa har sai lokacin da ta sadudua, ta bas hi damar lalata da ita.

Wannan ya sa ta kuwa garzaya wajen Jami’an tsaro ta kai kara ba tare da ya sani ba. A haka ne aka yi samame aka yi ram da shi a tube a wani otel mai suna Highbrow Estate da ke Garin Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel