Bidiyon cin hancin miliyan $5m: Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar a kan Ganduje

Bidiyon cin hancin miliyan $5m: Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar a kan Ganduje

A ranar Litinin ne reshen babbar kotun tarayya da ke Kano ya yi watsi da karar da wani lauya mai fafutikar kare hakkin bil'adama, Bulama Bukarti, ya shigar a gabanta dangane da zargin gwamna Ganduje da karbar cin hanci.

Bukarti ya garzaya neman kotun ta tilasta hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) a kan ta binciki zargin da ake yi wa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi umar Ganduje, na karbar cin hancin dalar Amurka miliyan $5, kamar yadda wani faifan bidiyo da aka wallafa a jaridar Daily Nigerian da kafafen sadarwa ya nuna.

Alkalin kotun, Jastis Obiorah Egwuatu, ya ce kotun ta yi watsi da karar ne saboda rashin gabatar da hujja daga bangaren mai kara.

A takardar karar da ya shigar, Bukarti ya bukaci kotun ta bayar da wani umarni da zai tilasta EFCC ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da kimiyyar zamani domin tabbatabar da cewa fuskar gwamna Ganduje ne a cikin faifan bidiyon ko akasin hakan.

Bidiyon cin hancin miliyan $5m: Kotu ta yi watsi da karar aka shigar da Ganduje

Ganduje
Source: Twitter

Ana zargin cewa gwamna Ganduje ne yake karbar cin hancin kudi daga hannun wasu 'yan kwangila a jihar Kano a cikin faifan bidiyon da aka fitar.

DUBA WANNAN: Tsoffin gwamnoni 6 na Arewa da kan iya fuskantar hukuncin da aka yanke wa Orji Kalu

Da kotun ke zartar hukunci ranar Litinin, Jastis Egwuatu ya bayyana cewa babu wata hujja mai karfi da mai kara ya gabatar domin jingina bukatarsa ta neman a bawa EFCC umarnin ta gudanar da bincike a kan faifan bidiyon ko kuma ta saki bayani a kansa.

Alkalin kotun ya kara da cewa ya kori karar ne saboda mai kara bai gabatar da wata shaida da ta nuna cewa hukumar EFCC tana da wani bayani da ya kamata jama'a su sani ba a kan faifan bidiyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel