Rundunar NAF ta yi luguden wuta a wurin taron ISWAP da Boko Haram a Kollaram

Rundunar NAF ta yi luguden wuta a wurin taron ISWAP da Boko Haram a Kollaram

- A ranar Litinin ne rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda rundunarta ta musamman ta markade 'yan ta'adda

- Ta tarwatsa 'yan ta'addan ISWAP da na Boko Haram a Kollaram da ke jihar Barno yayin da suke taro

- Shugabancin rundunar sojin ta tabbatar da cewa, zata kokarta wajen karasa ragowar 'yan ta'addan

A ranar Litinin ne rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda rundunarta ta musamman mai suna ‘Operation Rattle Snake’ da ke yankin Arewa maso Gabas ta yi wa ‘yan ta’adda luguden wuta. A cikin ranakun karshen mako ne rundunar ta musamman suka ragargaza ‘yan ta’addan ISWAP da Boko Haram a yayin taron da suka yi a Kollaram, jihar Barno.

Kamar yadda takardar da Air Commodore Ibikunle Daramola ya fitar ta ce, “A cigaban tabbatar da zaman lafiya, runduna ta musamman din ta markade wasu mayakan ISWAP a lokacin da suke taro a maboyarsu da ke Kollaram a yankin tafkin Chadi na arewacin jihar Barno.

DUBA WANNAN: Jarumi Adam A. Zango ya koma harkokinsa Kudancin kasar nan

“An aiwatar da wannan luguden wutar ne a ranar 14 ga watan Disamba 2019 bayan sahihan bayanan sirri da aka samu na taron shuwagabannin ISWAP din a yankin.

“Jirgin yakin NAF din sun hari yankin inda cikin nasara suka hallaka ‘yan ta’addan. Rundunar ta sha alwashin tarwatsa duk ragowar ‘yan ta’addan da ke yankin Arewa maso gabas din Najeriya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel