Ribas: Shekara daya da mutuwar O. B. Lulu-Briggs, ba a birne shi ba tukun

Ribas: Shekara daya da mutuwar O. B. Lulu-Briggs, ba a birne shi ba tukun

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa idan Ranar 27 ga Watan Disamban 2019 ta zo, an cika shekara guda kenan da rasuwar rikakken Attajirin nan da aka yi a jihar Ribas, O.B Lulu-Briggs.

Marigayi O.B Lulu-Briggs ya cika ne bara a Garin Accra ta kasar Ghana, amma kawo yanzu ba a dawo da gawarsa gida domin ayi masa jana’iza ba, kamar yadda aka san ‘Yan kabilar Kalabari.

Cif O.B Lulu-Briggs, Alkali ne wanda aka sani da kyauta a lokacin da ya ke raye. Sai dai rikici tsakanin Iyalin Mamacin ya sa har yanzu ba a rufe shi ba, shekara kusan guda kenan yanzu.

Daya daga cikin manyan ‘Ya ‘yan Marigayin, Dumo Lulu-Briggs, ya nemi ‘Yan sanda su yi bincike game da abin da ya kashe Mahaifinsu wanda ya cika Ranar 27 ga Watan Disamban 2018.

KU KARANTA: Ashe Mawaki Ado Gwanjo Mijin ta ce ne a cikin gida

Mai dakin da Marigayin ya bari ta yi masa takaba, Dr. Seinye Lulu-Briggs ta nemi ayi maza a bizne Attajirin. Wata da watanni da ta rubuta wannan wasikar, ba a bizne tsohon Mijin na ta ba.

A lokacin, Dr. Seinye Lulu-Briggs ta koka da yadda aka shafe watanni bakwai ba a bizne wannan Bawan Allah ba. Shekara guda za a cika a makon gobe babu labarin birne Marigayi Cif Briggs.

Rahotanni sun ce Dumo Lulu-Briggs ya na fada da Kishiyar Mahaifiyarsa ne saboda abin Duniya. Majiyar jaridar ta ce sha’anin raba gadon da aka bari ne babban abin da ya raba gidan Marigayin.

Tsofaffin shugabannin kasar nan irin su Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun yi kokarin sasanta sabanin da aka samu a gidan Cif Lulu-Briggs, amma abin ya ci tura har zuwa yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel