Yaki da rashin gaskiya: Buhari bai kai wa ga ci – Inji Usman Bugaje

Yaki da rashin gaskiya: Buhari bai kai wa ga ci – Inji Usman Bugaje

Tsohon Mai ba shugaban kasa shawara a Najeriya, Dr. Usman Bugaje, ya fahimci akwai matsala a irin tsarin tafiyar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yaki da rashin gaskiya.

Usman Bugaje ya bayyana yakin da gwamnatin nan ta ke yi da marasa gaskiya da matukar abin kunya. Dattijon ya kuma zargi Miyagun ‘Yan siyasa da hannu a rikicin Makiyaya da Manoma.

Dr. Bugaje ya ke cewa wasu ‘Yan siyasan kasar nan da ba su da hanyar lashe zabe sai ta hada al’umma fada da sunan addini da kabilanci ne su ke ruruta wutar fadan Makiyaya da Manoma.

Bugaje ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi wani jawabi wajen bikin taya Sarkin Fulanin Legas, Dr. Mohammed Abubakar Bambado II murnar shafe shekaru 25 a kan gadon sarauta.

KU KARANTA: Jarumi Adam Zango ya koma harkokinsa a Garin Legas

Yaki da rashin gaskiya: Buhari bai kai wa ga ci – Inji Usman Bugaje

Usman Bugaje ya na ganin babu nasara a yaki da rashin gaskiyan Buhari
Source: UGC

Tsohon ‘Dan majalisar wakilan tarayyar kasar da ya wakilci Kaita da Jibiya ya gabatar da takarda ne mai taken Najeriya a lokacin wahala; hanyar kai wa ga zaman lafiya da hadin kan kasa.

Wadanda su ka samu halartar wannan biki da aka shiryawa Sarkin Fulanin na Legas sun hada da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, da kuma Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

A jawabinsa, Bugaje ya koka da halin da ake ciki yanzu na rashin aikin yi, ya ce idan ba a tunkari yadda za a kula da yawan al’ummar kasar ba, Najeriya za ta samu kan ta a cikin wani mugun hali

Tsohon ‘Dan takarar gwamnan na Katsina ya ke cewa dole jama’a su damu ganin an gaza cin yakin da barayi. “Yaki da rashin gaskiyar da ake yi, akalla ka ce ya ba mu matukar kunya”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel