Toh fa! Malaman jami’ar OAU guda 3 sun mutu a cikin kwanaki 10

Toh fa! Malaman jami’ar OAU guda 3 sun mutu a cikin kwanaki 10

Kungiyar malaman jami’a, ASUU, reshen jami’ar Obafemi Awolow dake garin Ile Ife na jahar Osun ta shiga halin alhini da jimami a sanadiyyar mutuwar malamansu guda uku a cikin kwanaki 10.

Jaridar Punch ta ruwaito malamar da ta mutu ta baya bayan nan ita ce Dakta Victoria Adeniyi, shugaban sashin koyar da wasan kwaikwayo na jami’ar, wanda ta mutu a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Yansanda sun kama Sojan Najeriya da aikata halin bera a jahar Edo

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran malaman da suka fara mutuwa kafin mutuwar Victoria sun hada da Dakta Nicholas Igbokwe wanda aka tsinci gawarsa a cikin ofishinsa a ranar Juma’a ta sama da ta gabata, sai kuma Farfesa Jerome Elusiyan wanda yan bindiga bindige shi a ranar 13 ga watan Disamba.

Mai magana da yawun hukumar jami’ar, Abiodun Olanrewaji ya bayyana cewa: “Kasa da sa’o’i 48 da mutuwar Farfesa Jerome Elusiyan a hannun yan bindiga sai kuma muka sake tafka wani babban rashin, na Dakta Victoria Adeniyi.

“Sai dai tuni shugaban jami’ar wanda ya bayyana damuwarsa da yadda Victoria ta mutu ya bada umarnin a gudanar da binciken gawarta domin tabbatar da musabbabin mutuwarta.” Inji shi.

Shi ma a jawabinsa, shugaban kungiyar malamai reshen jami’ar OAU, Adeola Egbedokun ya bayyana mutuwar mamatan a matsayin wani lamari mai tsananin tayar da hankali, kuma ya jefasu cikin halin jimami da alhini.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai samame kauyen Sukuku dake cikin karamar hukumar Kwali na babban birnin tarayya Abuja inda suka kashe wani bawan Allah, sa’annan suka yi awon gaba da dansa.

Wani mazaunin garin ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace a ranar Alhamis da ta gabata yan bindigan da yawansu ya kai 20 suka afka cikin garin suna ta harbe harben mai kan uwa da wabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel