Gwamnati za ta iya hukunta kamfanin da ke raba wuta a Enugu da Fatakwal

Gwamnati za ta iya hukunta kamfanin da ke raba wuta a Enugu da Fatakwal

Shida daga cikin kamfanoni takwas masu raba wutar lantarki a Najeriya da hukumar NERC ta ke tunanin karbe lasisinsu, sun tsallake fushin gwamnati bayan an yi wani bincike a kansu.

Mafi yawan kamfanonin wutan za su cigaba da aiki bayan bincike ya nuna za a kyale masu lasisinsu. Amma dai akwai yiwuwar a hukunta kamfanin raba wutan da ke Enugu da Fatakwal.

A wani jawabi da hukumar NERC ta fitar a Ranar 12 ga Watan Disamban 2019, NERC ta kira wani zama a Ranar Alhamis domin sauraron shugabannin wadannan manyan kamfanonin wutan.

Hukumar ta NERC mai kula da harkar wutan lantarki a Najeriya za ta kuma yi wani zaman sirri da shugabannin sauran kamfanoni da ke raba wuta a kasar, bayan sun samu an yi masu lamuni.

KU KARANTA: An yi wa Likitoci da Marasa lafiya fashi a cikin asibiti

NERC ta dagawa kamfanonin kafa ne bayan sun iya badan rahoton MRO a watanni ukun nan. Gwamnati ta yanke hukuncin cewa ba za a karbe masu lasisi ba, amma za a sake zama da su.

Kwamishinan hukumar NERC, Dafe Akpeneye, ya bayyana cewa daga cikin kamfanoni takwas da su ka gabatar da takardunsu, EEDC da PHEDC ne ba su cika sharudan da aka gindaya ba.

Akpeneye ya bayyana cewa an bukacin kamfanonin su bada gamsasshen rahotonsu na daya daga cikin a watannin Yuli zuwa Satumba domin a duba yiwuwar ba su damar cigaba da aikinsu.

Kamfanonin EEDC da PHEDC za su yi wa NERC bayani a bainar juma’a a Abuja. Sauran kamfanonin da aka dagawa kafa sun hada da na Abuja, Benin, Ikeja, Kano, Yola da Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel