Yansanda sun kama Sojan Najeriya da aikata halin bera a jahar Edo

Yansanda sun kama Sojan Najeriya da aikata halin bera a jahar Edo

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo sun kama wani jami’in rundunar Sojan Najeriya, Eyosu Kennedy mai shekau 25 da laifin tafka halin bera bayan ya saci wata mota kirar Toyota Camry.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito jami’in Sojan mai mukam Private yana aiki ne a bataloya ta 112 dake jahar Borno, kuma an gabatar da shi ga yan jaridu ne a sakariyar Yansandan Najeriya dake garin Bini na jahar Edo.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutumi, sun tafi da dansa a Abuja

Kwamishinan Yansandan jahar, Lawan Tanko Jimeta ya bayyana cewa Sojan ya sace motar ne daga babban birnin tarayya Abuja, inda ya kai ta jahar Edo domin ya sayar da ita, dubunsa ta cika ne a daidai lokacin da yake kokarin sayar da motar.

Sai dai a nasa bangaren, Sojan ya musanta satar motar, inda yace sayota ya yi daga wajen wani jami’in hukumar kwastam a garin Abuja. “A shekarar 2016 na shiga aikin Soja, na samu izinin zuwa jahar Edo ne, amma kafin na taho wani mutum ya sayar min da motar tun a Maiduguri.

“Mutumin yace min shi jami’in kwastam ne, kuma zai sayar da motar a kan N500,000, sai na fada masa N100,000 ne a hannuna, amma idan an biyamu albashi a karshen wata zan cika masa N400,000. A kan haka muka killa ciniki, na bashi N100,000, shi kuma ya bani motar.

“Bayan na shigo Bini da motar sai ta samu matsala, daga nan sai na kai ta wajen gyara, inda bakaniken dake gyaran motar ya nemi na sayar masa da motar, ni kuma na amince, amma koda ya tambayeni na bashi takardun motar, sai na fada masa bani da su.” Inji shi.

Daga nan sai bakaniken ya hada shi da wani dansanda da yace zai sayi motar, amma dansandan ya matsa masa ya bashi takarda, shi kuma yace masa babu, daga nan aka tsananta bincike har aka gano wasu takardun mota a cikin motar, da aka kira lambar dake cikin takardun sai wani mutumi ya tabbatar musu motarsa ce aka sace daga Abuja.

Daga karshe kwamishinan Yansandan jahar ya bayyana cewa za su gurfanar da jami’in Sojan da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel