Masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutumi, sun tafi da dansa a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutumi, sun tafi da dansa a Abuja

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai samame kauyen Sukuku dake cikin karamar hukumar Kwali na babban birnin tarayya Abuja inda suka kashe wani bawan Allah, sa’annan suka yi awon gaba da dansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin ne ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda yace a ranar Alhamis da ta gabata yan bindigan da yawansu ya kai 20 suka afka cikin garin suna ta harbe harben mai kan uwa da wabi.

KU KARANTA:Yan bangan siyasa sun harbe kananan yara guda biyu a yayin gangamin siyasa

“Kai tsaye yan bindigan suka zarce shagon da yaron ke cajin waya, inda suka nemi ya kaisu dakin mahaifinsa, inda yaron ya bayyana musu cewa mahaifinsa baya gida, amma sai suka yi barazanar kashe shi idan bai kai su ba.

“Daga nan ne sai yaron ya garzaya dasu zuwa dakin mahaifin nasa, amma koda mahaifin ya hangi yan bindigan sun nufo dakinsa, sai ya yi kokarin tserewa ta kofar baya, a daidai wannan lokaci ne yan bindigan suka bude masa wuta, nan take ya fadi matacce, sa’annan suka tsere tare da tafiya da dansa.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani daga cikin iyalan mamacin ya tabbatar da yan bindigan sun tuntubesu a kan yaron da suka yi awon gaba da shi, inda yace suna neman kudin fansa naira miliyan 1 daga hannunsu.

“Da farko sun nemi mu basu naira miliyan 5 ne, amma daga bisani bayan ciniki ya zurfafa, sun amince a kan naira miliyan 1, a yanzu tashin hankalinmu shi ne yadda zamu tara wadannan makudan kudi.” Inji shi.

Daga karshe mutumin ya bayyana cewa tuni an yi ma mamacin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin Yansanda Abuja, Marian Yusuf game da lamarin ya ci tura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel