DSS: Ana zargin Sowore da aiki da ‘Yan Boko Haram, IPOB, da Shi’a

DSS: Ana zargin Sowore da aiki da ‘Yan Boko Haram, IPOB, da Shi’a

Wata Majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi wa Yele Sowore wanda ya ke a garkame tambayoyi a game da zargin alakarsa da 'Yan ta’addan Boko Haram da wasu kungiyoyi.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa zargin hannu a cikin tafiyar Boko Haram ya na cikin sababbin zargin da ake jifan Omoyele Sowore da su. A makon jiya ne aka sake damke Sowore.

“Jami’an tsaro su na ta faman tambayarsa game da alakarsa da Boko Haram, kungiyar Shi’ar Najeriya ta IMN da kuma kungiyar IPOB mai fafutukar neman ‘yancin kasar Biyafara.”

A cewar Majiyar, irin wannan tambayoyi ne aka yi wa Sowore a Ranar 12 ga Watan Nuwamban bana. Lauyoyin sa sun ce ana binsa da wannan zargi ne domin a samu hanyar cigaba da tsare sa.

KU KARANTA: DSS ta saki Sowore bayan kwanaki fiye da 100 a daure

DSS: Ana zargin Sowore da aiki da ‘Yan Boko Haram, IPOB, da Shi’a
Watakila a sake gurfanar da Sowore a gaban kotu
Source: UGC

A Nuwamban shekarar 2013, gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta sa sunan kungiyar Boko Haram cikin ‘Yan ta’addan Duniya. Daga baya kungiyar ta yi kaurin suna wajen ta’addanci.

Rahotannin sun ce Sowore ya na ta cigaba da nuna cewa bai da alaka da kungiyoyin. An samu wannan bayani ne kwanaki kusan goma da jami’an DSS su ka sake cafke ‘Dan gwagwarmayar.

Tambayoyin da jami’an tsaron su ke yi wa tsohon ‘Dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa akwai yiwuwar a gabatar da shi a kotu gaban Alkali bisa zargin hannu wajen aikin ta’addanci.

Inibehe Effiong, wanda ya na cikin Lauyoyin da ke kare Sowore a kotu ya bayyana cewa ba yanzu aka fara kokarin jifarsa da wannan zargi ba, a baya an bincikesa a kan haka, ba a samu komai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel