Dubun wasu gungun dakarun Sojin Najeriya masu garkuwa da mutane ta cika

Dubun wasu gungun dakarun Sojin Najeriya masu garkuwa da mutane ta cika

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo ta samu nasarar cafke wasu gungun dakarun rundunar Sojin Najeriya dake da hannu cikin satar mutane, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Jaridar Pulse ta ruwaito Yansanda sun kama Sojojin ne tare da wani abokin aikinsu farar hula, inda suka tabbatar ma Yansanda cewa su ne suke fitinar jama’an garuruwan Agenebode, Fugar da sauran sassan jahar.

KU KARANTA: Yan bangan siyasa sun harbe kananan yara guda biyu a yayin gangamin siyasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen sojojin kamar haka; Collins Ameh mai mukamin kofur dake aiki a rundunar Sojan kasa ta uku dake Jos, Balogun Taiwo mai mukamin Las kofur dake Bataliya ta 35 dake Katsina da Evans Isibor mai mukamin Private daga Artillery Brigade Owerri, amma yana aiki a Borno sa kuma abokin aikinsu Goodluck Igebenebor.

Sojojin sun sace wani mutumi ne mai suna Joseph Otono a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2019 a garin Fugar, inda daga bisani suka sakeshi bayan yan uwansa sun biya kudin fansa. Haka zalika Otono ya yi garkuwa da Mohammed Hassan a Agenebode a ranar 14 ga watan Oktoba.

Da yake tabbatar da kama miyagun Sojojin, kaakakin rundunar Yansandan jahar Edo,DSP Chidi Nwabuzo ya bayyana cewa tuni suna hannunsu, kuma bincike ya zurfafa a kansu da abokin ta’asarsu.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai samame kauyen Sukuku dake cikin karamar hukumar Kwali na babban birnin tarayya Abuja inda suka kashe wani bawan Allah, sa’annan suka yi awon gaba da dansa.

Wani mazaunin garin ne ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda yace a ranar Alhamis da ta gabata yan bindigan da yawansu ya kai 20 suka afka cikin garin suna ta harbe harben mai kan uwa da wabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel