Kisan jami'an kungiyar agaji: Ya kamata gwamnatin tarayya ta canza salon tattaunawa da yan ta'adda - ACF

Kisan jami'an kungiyar agaji: Ya kamata gwamnatin tarayya ta canza salon tattaunawa da yan ta'adda - ACF

Kungiyar mashawartan Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta baiwa shugaba gwamnatin tarayya shawara ta canza salon tattaunawa da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP.

Kungiyar ta yi tsokaci kan kisan ma'aikatan agaji da jinkai ta Action Against Hunger (AAH) da yan ta'addan ISWAP sukayi a makon da ya gabata inda tayi kira ga gwamnati ta kara himma wajen ceto wadanda ke hannun yan ta'addan.

A jawabin da kakakin ACF, Muhammad Ibrahim ya saki, ya bayyana cewa abinda yan ta'addan sukayi ya sabawa koyarwan addinin Musulunci.

Ya bayyana cewa ikirarin gwamnati na cewa tana tattaunawa da kungiyoyin kasashen ketare wajen ceto wadanda aka sace bai haifi da mai ido ba.

Mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar daular addinin Musulunci a yankin Afrika ta yamma ISWAP sun hallaka ma'aikatan kungiyar jinkai da tallafin Action Against Hunger da suka sace tun watar Yulin 2019.

Zaku tuna cewa yan ta'addan ISWAP sun kashe direba sannan suka sace ma'aikatan kungiyar AAH a Damasak, jihar Borno.

Hakan ya biyo bayan kisan Saifur Ahmed, ma'aikaciyar UNICEF da Hauwa Liman da Boko Haram sukayi a watan Oktoban, 2018.

Dan jarida Ahmed Salkida ya ce yan ta'addan sun hallaka mutanen ne saboda rashin cika alkawari na gwamnatin tarayya.

Tun watan Maris na 2018 da gwamnatin tarayya ta samu nasarar ceto yan matan Dapchi daga hannun yan Boko haram ta hanyar yarjejeniya, har yanzu ba'a sake cimma matsaya don ceto rayukar sauran mutanen ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel