Tsoffin gwamnoni 6 na Arewa da kan iya fuskantar hukuncin da aka yanke wa Orji Kalu

Tsoffin gwamnoni 6 na Arewa da kan iya fuskantar hukuncin da aka yanke wa Orji Kalu

A ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba, ne wata babbar kotun tarayya ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, hukuncin daurin shekaru 12 a kurkuku bayan samunsa da laifin karkatar da fiye da biliyan N7 daga asusun jihar Abia.

Kafin wannan hukuncin, a baya wasu kotunan sun yanke kusan irin wannan hukunci a kan Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato, da Joly Nyame, tsohon gwamnan jihar Taraba.

A halin yanzu akwai tsofin gwamnoni da dama da ake tuhumarsu da laifin cin hanci a gaban kotuna daban-daban. Daga cikinsu akwai wadanda alamu ke nuna cewa zasu iya fuskantar irin hukuncin da ya fada a kan Kalu.

Sule Lamido: Tsohon gwamnan jihar Jigawa ne daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin jami'iyyar PDP.

Am gurfanar da shi a gaban kotu, tare da 'ya'yansa, bisa tuhumar cin hanci, lamarin da yasa har aka ajiye su a gidan gyaran hali na Kurmawa dake birnin Kano. Har yanzu kotu bata yanke hukunci na karshe a kan tuhumar da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan da 'ya'yansa ba.

Murtala Nyako: Tsohon sojan sama, Murtala Nyako, ya mulki jihar Adamawa har sau biyu kafin majalisar dokokin jihar Adamawa ta tsige shi kafin karewar wa'adinsa.

EFCC ta gurfanar da Nyako tare da dan cikinsa, Sanata Abdulaziz Nyako, tare sauran wasu mutane 7 bisa tuhumarsu da aikata laifuka 37 da suka hada da almundahana, sata, cin amana, cin hanci da sauransu.

Hukumar EFCC tana zargin tsohon gwamnan tare da sauran mutanen da wawure kudi da yawansu ya kai biliyan N29.

DUBA WANNAN: Fasto ya yi wanka a coci, jama'a sun shanye ruwan

Saminu Ibrahim Turaki: Saminu Turaki, kamar yadda aka fi kiransa, shine ya mika wa Sule Lamido, mulkin jihar Jigawa a shekarar 2007.

Turaki yana cikin sahun jerin gwamnonin da EFCC ta fara gurfanar wa bayan sun bar gwamnati har ma kotu ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari.

An fara gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2011 kafin daga bisani a sake gurfanar da shi shekarar 2017 bisa tuhuma 32 da suka da karkatar da biliyan N36 daga asusun jihar Jigawa kuma har yanzu ba a yanke masa hukunci ba.

Babangida Aliyu: Ya zama gwamnan jihar Neja a karo na farko a shekarar 2007 kafin a sake zabensa a karo na biyu a shekarar 2011.

Ana tuhumarsa tare da Umar Nasco, tsohon shugaban ma'aikatan jihar Neja, da tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Tanko Beji, da wawurar biliyan N2 daga asusun jihar Neja.

An yi zaman kotu na karshe a kan karar da EFCC ta shigar da su a ranar 7 ga watan Nuwamba, 2019.

Jonah Jang: An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Filato kuma tsohon sanata, Jonah Jang, tare da Yusuf Pam, ma'aikaci a ofishin sakataren gwamnatin Filato.

Hukumar EFCC tana tuhumarsu da laifuka 12 da suka hada da waske wa da kudi, biliyan N6.3.

An yi zaman kotu na karshe a kan tuhumar da ake yi wa Jang a ranar 4 ga watan Nuwamba.

Gabriel Suswam: A zaben shekarar 2019 ne tsohon gwamnan jihar Benuwe, Gabriel Suswan, ya lashe kujerar Sanatan jihar Benuwe ta arewa maso gabas duk da zargin cin hanci dake rataye a wuyansa.

A shekarar 2015 ne EFCC ta fara gurfanar da Suswan a gaban kotu tare da kwamishinansa na kudi, Omadachi Okulobi, bisa tuhumarsu da karkatar da biliyan N3.1 daga asusun jihar Benuwe.

A watan Yuli, 2019, alkalin dake sauraron karar Suswan tun 2015 ya sanar da janyewarsa daga karar bayan an zarge shi da hada baki da tsohon gwamna Suswan domin tauye adalci.

An fara sabuwar tuhuma a kan Suswan a gaban kotun mai Shari'a, Jastis Okon Abang, da ke Abuja a watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel