Asibiti: 'Yan fashi da makami sun yi wa majinyata da ma'aikatan asibiti fashi

Asibiti: 'Yan fashi da makami sun yi wa majinyata da ma'aikatan asibiti fashi

Wasu 'yan fashi da makami sun kai hari wani asibiti a jihar Ogun inda suka yi wa majinyata da ma'aikata fashi. 'Yan fashin sun kai farmaki ne ga wani asibitin kudi a Ibafo da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun. Sun kwace dukiyoyin majinyata da dama.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce 'yan fashi da makamin sun hari asibitin ne inda suka saka tashin hankula ga majinyata, 'yan uwansu da ma'aikata.

Ya shaida cewa, a ofishin hukumar na Ibafo, an samu kiran neman dauki inda DPO Abiodun Ayinde ya jagoranci runduna ta musamman zuwa asibitin.

Tuni 'yan fashin suka ranta a na kare tare da neman mafaka a daji bayan ganin 'yan sandan da suka yi.

DUBA WANNAN: Fasto ya yi wanka a coci, jama'a sun shanye ruwan

Oyeyemi yace, 'yan sandan basu saurara ba don kuwa bin 'yan fashin suka yi. Sun cafkesu a maboyarsu da ke Shamawa a karamar hukumar Sagamu da ke jihar.

Ya bayyana sunayen 'yan fashin da: Folarin Azeez wanda aka fi sani da Hyper mai shekaru 25, Temitope Bolariwa wanda aka fi sani da Tincan mai shekaru 24 da Kolade Ahmed mai shekaru 30. Ya kara da cewa, an samu wayoyi 12 a hannunsu tare da agogunan hannu masu yawa wadanda daga bisani aka ba masu su.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce, a lokacin da ake cigaba da bincike, an gano wani fashi da wadanda ake zargin suka yi.

A halin yanzu, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin mika wadanda ake zargin ga sashi na musamman na binciken laifukan fashi da makami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel