Gwamnan Borno ya yi kira ga Buhari yayi hattara da wasu gwamnonin Arewa 3 - Majiya

Gwamnan Borno ya yi kira ga Buhari yayi hattara da wasu gwamnonin Arewa 3 - Majiya

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya fasa kwan yunkurin da gwamna El-Rufai, Fayemi, Bagudu da Badaru, keyi na kwace akalan jam'iyyar ne saboda daya daga cikinsu ya zama shugaban kasa a 2023, ta hanyar tsige Oshiomole saboda zai iya zama musu cikas.

Zulum yace abinda aka sanar da su shine shugaba Buhari na bukatar zama dasu kan wasu lamuran shugabancin al'ummarsu, ashe El-Rufa'i ne ya shirya ganawar tare da abokansa.

Majiya da ke da labarin abinda ya faru cikin ganawar ya bayyana cewa Zulum ya yi kira ga shugaba Buhari yayi hattara da wadannan gwamnonin hudu.

Ya fadawa shugaban kasa cewa El-Rufa'i da abokan shirya tuggunsa na yin haka don moriyar kansu ne ba na jam'iyya ba.

Zulum ya fallasa cewa gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya taba rokansa ya goyi bayan tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari, domin maye gurbin Oshiomole idan an cireshi. Ya kalubalanci Bagudu ya karyata idan ba haka bane.

Majiyar ruwaito Zulum ya ce: "Mai girma shugaban kasa, ka ga wadannan gwamnonin masu son cire Oshiomole, suna yi ne don son zama shugaban kasa a 2023. Wai shin sai mun rusa jam'iyyar don muna son zama shugaban kasa ne? Gaskiya mubi a hankali."

"Na yi imanin cewa shugaban jam'iyya na adalci. Ban taba haduwa da shi ba, amma ya bari aka bi gaskiya wajen zaben fidda gwanin da na zama dan takarar APC a jihar Borno. Hakazalika bai taba tambayata wata alfarma ba."

A wani labarin mai alaka, Tsohon dan takaran gwamnan Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa wasu gwamnoni na kokarin tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Adams Oshiomole domin daura tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari.

Yayinda yake magana da manema labarai a jihar Zamfara, Marafa yace gwamnonin na shirya hakan ne don kwace jam'iyyar domin siyasar 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel