Fasto ya yi wanka a coci, jama'a sun shanye ruwan

Fasto ya yi wanka a coci, jama'a sun shanye ruwan

- Bidiyon wani fasto yana wanka a cikin coci kuma mabiyansa na shan ruwan wankan ya jawo cece-kuce

- A bidiyon mai tsawon mintuna uku, an ga faston sanye da bantai kuma yana ninkaya cikin kwatanniya a cocin

- Ya sanar da mabiyansa cewa Ubangiji ne ya umarcesa da yin hakan kuma zasu samu tabaraki matukar suka sha

Bidiyon wani fasto yana wanka a majami’a kuma yana shayar da mabiyansa ruwan wankan, ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani. Hakan kuwa ya jawo cece-kuce daga jama’a da dama.

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna uku, faston dan asalin kasar Ghana wanda har yanzu ba a gano sunansa ba, ya bayyana da bantai kuma yana ninkaya a cikin ruwan da ke kwatanniya a cikin majami’ar.

An ga mabiyan sun yi layi suna shan kofi daddai daga ruwan wankan bayan da faston ya gama musu jawabi.

DUBA WANNAN: Aiyukan alherin marigayi Sani Abacha da kwata - kwata ba a maganarsu

Kamar yadda jaridun yankin suka ruwaito, Ubangiji ne ya umarcesa da ya yi hakan. Kamar yadda yace, duk wanda ya sha daga wannan ruwan, Ubangiji zai kara albarkatarsa.

A lokacin da aka samu wannan rahoton, ba a sanar da lokacin da abun ya faru ba, amma an bada sunan majami’ar . Sunan ta ‘Endtime Church Of Nation’.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel