Barazanar Ma’aikata ta sa Jihohi su na fadi-tashi a game da karin albashi

Barazanar Ma’aikata ta sa Jihohi su na fadi-tashi a game da karin albashi

Bayan barazanar kungiyar ‘Yan kwadagon Najeriya na cewa ba za ta iya shawo kan ‘Ya ‘yanta idan aka gaza karkare yarjejeniyar karin albashi ba, gwamnoni su na kokarin risker wa’adi.

Kungiyar NLC ta bada daga nan zuwa Ranar 31 ga Watan Disamban 2019 domin a kammala maganar fara biyan sabon tsarin albashi a jihohi. Bincike ya nuna jihohi kusan 30 sun tashi tsaye.

Wata jarida ta bayyana cewa a jihar Filato, magana ta yi nisa a kan soma biyan kowane ma’aikaci akalla N30, 000 duk wata. Sai dai gwamnan jihar bai fadi lokacin da za a fara biyan kudin ba.

A jihar Ekiti inda Gbenga Olowoyo ya ke matsayin Sakataren kwamitin da ke duba sha’anin karin albashin, ana sa rai a kammala duk wani zama kafin ranar karshen na Watan Disamban nan.

Olisa Ifejika wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na jihar Delta, ya shaidawa jaridar cewa gwamnatin Ifeanyi Okowa za ta biya ma’aikata duk abin da gwamnatin tarayya ta yanke a kasar.

KU KARANTA: An zabi wasu Gwamnoni da za su zauna da Gwamnati kan batun albashi

A jihar Enugu, Sakataren gwamnatin jihar, Simon Ortuanya, wanda shi ne ke jagorantar bangaren gwamnati a zaman karin albashin ya nuna cewa su na kan sawu guda da ‘Yan kwadagon jihar.

A makwabta jihar Abia, Mai girma gwamna Okezie Ikpeazu ya yi kira ga kwamitin da ya kafa a karkashin HOS Onyi Wamah ya kawo masa hanyar da duk da za a bi, a karawa ma’aikata albashi.

Kwamishinan yada labaran Imo, Felix Ebilikwe, ya ce kwanan nan gwamna Emeka Ihedioha zai rantsar da kwamitin da za su yi aikin karin albashin domin ganin ma’aikatan jihar sun ji dadi.

A jihar Ribas, ba a san halin da ake ciki a kan wannan batu ba. Kungiyar NLC ta ce ta aikawa gwamnan jihar takarda domin ta kafa kwamiti kan karin albashin. Kawo yanzu ba ayi hakan ba.

A jihar Osun ma babu wani labari kwakkwara game da shirin fara biyan wannan sabon tsarin albashi. Mun kuma ji cewa irin wadannan kwamiti bai fara aiki a jihohin Ogun da Benuwai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel