2023: Za mu yi magana game da takarar Tinubu idan lokaci ya yi – APC Legas

2023: Za mu yi magana game da takarar Tinubu idan lokaci ya yi – APC Legas

A wata hira da aka yi da shugaban jam’iyyar APC na jihar Legas, Tunde Balogun, ya nuna rashin goyon bayansu ga kiran da ake yi na sauke Adams Oshiomhole tare da tabo batun zaben 2023.

Da aka tambayi Alhaji Tunde Balogun a kan kishin-kishin din takarar tsohon gwamna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa sai ya nuna cewa rade-radin jama’a ne kurum wannan.

“A lokacin da ya fi dacewa, zan yi magana a kan wannan batu. Balogun ya cigaba da cewa: “Yanzu ya yi wuri mu fara magangunu a kan wannan lamari domin har yanzu babu tabbacin maganar.”

Da aka sake tambayar shugaban jam’iyyar game da mika takara zuwa Kudu maso Gabas sai ya ce: “Haka zalika, babu wani mataki da aka dauka tukuna a nan, duk abin da ake fada, jita-jita ce.”

KU KARANTA: Ambode ya saki layin Tinubu da Fashola - Shugaban APC

“Lokaci zai zo da za a san halin da ake ciki. Lokacin da za a fara magana a kan abin da zai faru a shekarar 2023 bai yi ba tukuna.” Balogun ya nemi a dakata da wannan magana zuwa nan gaba.

Tunde Balogun ya karyata abin da wasu ke fada na cewa mutum ba zai iya zama wani babba a siyasar Legas ba, har sai ya san Asiwaju Bola Tinubu. Balogun ya ce sam ba haka abin ya ke ba.

“Mafi yawan ‘Ya ‘yan jam’iyya ne su ka zabi shugaban jam’iyyar mu a kan wa’adin shekaru hudu a ofis, kuma shekara guda kurum ya shafe amma wasu fusatattun' Ya 'ya sun fara kiran ya sauka.”

A game da Oshiomhole, Balogun ya kara da cewa: “Su na son ya yi murabus ne saboda son ransu. Oshiomhole mutum ne wanda zai iya yin kuskure, don haka a kyale sa ya yi shekarunsa a ofis”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel