Kaucewa manufofin APC ya sa mu ka hana Ambode tikitin APC a 2019 - Balogun

Kaucewa manufofin APC ya sa mu ka hana Ambode tikitin APC a 2019 - Balogun

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Legas, Alhaji Tunde Balogun, ya yi hira da wani ‘Dan jarida kwanan nan, inda ya tabo batun siyasar APC a 2019 da wasu muhimman batutuwa a jihar Legas.

Da farko Tunde Balogun ya nuna cewa gwamna mai-ci Babajide Sanwo-Olu ya soma aiki da kyau domin ya fara gyaran wasu hanyoyin jihar, bugu da kari kuma ya fara sababbin aikace-aikace.

Alhaji Balogun ya bayyana cewa Akinwumi Ambode ya soma bin tafarkin da Bola Tinubu da Babatunde Fashole su ka bi, amma daga baya ya yi watsi da tsarinsu, ya kama wani layi dabam.

Shugaban jam’iyyar mai mulki ya bayyana cewa kaucewa daga muradun jam’iyyar APC wanda ta faro tun daga AD a 1999 shi ne babban abin da ya jawo Ambode ya rasa tikitin APC a bara.

“Lokacin da Bola Tinubu ya ke nan, ya yi aiki sosai a harkar sufuri, kiwon lafiya da ilmi. Da Babatunde Fashola ya zo, sai ya cigaba da tsare-tsaren, ya kawo cigaba, don haka ya zarce.”

KU KARANTA: Tinubu ya samu Digirin girmamawa daga Jami'ar IBB a Neja

Kaucewa manufofin APC ya sa mu ka hana Ambode tikitin APC a 2019 - Balogun

APC ta hana Akinwumi Ambode tikitin APC domin ya nemi tazarce
Source: UGC

“Yayin da Akinwumi Ambode ya karbi mulki, da farko ya na bin tsare-tsaren jam’iyya, amma bayan wani lokaci sai ya kauce hanya. Wannan shi ne babban kuskuren da ya hana sa tazarce.”

Balogun ya jero yadda tsohon gwamna ya saki layi da cewa: “Kazanta ta bi ta cika Legas. A bangaren hanyoyi, ramuka su ka cika titi, yayi watsi da manyan titunan da Fashola ya soma”

“Ya yi watsi da ayyukan gwamna Fashola wadanda su ka hada da manyan tituna da layin dogo daga Mile 12 zuwa Badagry. Akwai gidajen da ake ginawa a Ilubirin da tsarin tattara bola.”

Shugaban na APC ya kara da cewa: “Wannan ba su cikin tsarinmu, mun shirya hanyar tattara bola. Dole mu ka jira lokaci ya yi, mu ka yi abin da ya dace domin kawowa jihar Legas cigaba”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel