Tinubu, Marigayi Kure da Zukogi sun samu kyautar Digiri a IBBUL

Tinubu, Marigayi Kure da Zukogi sun samu kyautar Digiri a IBBUL

Jami’ar Ibrahim Badamasi Babaginda da ke Lapai a jihar Neja, ta bada Digirin girmamawa ga wasu manya da su ka hada da Bola Ahmed Tinubu da Marigayi tsohon gwamnan jihar Neja.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Jami’ar jihar Nejar ta karrama Jagoran jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Digirin da ake kira Doctor of Letters ko kuma Honoris Cauda.

Haka zalika an ba Marigayi Injiniya Abdulkadir Kure Digirin Dakta a fagen kimiyya (Sc.D.) na girmamawa. Abdulkadir Kure ya rasu ne a farkon 2020, kusan shekaru uku kenan da su ka wuce.

Marigayi tsohon gwamnan haifaffen Garin Lapai ne inda wannan Jami’a ta ke. Har ila yau Makarantar ta karrama tsohuwar Alkalin Alkalan jihar, Mai shari’a Maria Sanda Zukogi da LLD.

An yi wannan ne a bikin yaye ‘Daliban jami’ar da aka shirya a Ranar Asabar 14 ga Watan Disamba, 2019. Wannan shi ne karo na uku da aka yaye wadanda su ka kammala Digiri a jami'ar.

KU KARANTA: Tinubu ya hadu da Atiku Abubakar da Gwamnan Adamawa

Shugaban jami’ar wanda ke shirin barin kujerarsa, Farfesa Muhammad Nasir Maiturare, ya shaida cewa Dalibai 3, 212 su ka kammala karatu daga makarantar a zangon 2017/18 da 2018/19.

Daga cikin wadanda aka yaye an samu mutum 23 da su ka fita da matakin Digiri na farko 23. Akwai Dalibai 700 da su ka samu rukuni na Digirin 2’1, sannan 1, 999 su ka tashi da 2’2.

Sauran Daliban 499 sun gama ne da matakan Digiri na karshe kamar yadda Farfesa Maiturare ya bayyana. Yansahwu Adio da Maryam Gomina ne su ka gama da sakamakon da ya fi kyau.

Yansahwu Adio wanda yanzu haka ya ke yi wa kasa hidima a Legas ya kammala Digiri a harshen Faransaci ne da maki 4.73 cikin 5 kamar dai Maryam Gomina wanda aka yaye a sashen kimiyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel