Imo: Abin da ya sa ‘Yan Sanda su ka cafke fitaccen Mawaki Duncan Mighty

Imo: Abin da ya sa ‘Yan Sanda su ka cafke fitaccen Mawaki Duncan Mighty

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na reshen jihar Imo sun bayyana dalilin da ya sa su ka kama Mawakin nan mai suna Duncun Mighty. Jami’an sun sace ana zarginsa ne da laifin tafka zamba.

Da farko wani Attajirin Abokin Mawakin ya fito ya shaidawa Duniya cewa wasu ‘Yan bindiga ne su ka sace Duncan Mighty. Jami’an tsaron kasar sun yi karin haske game da duk abin da ya faru.

A Ranar Asabar 14 ga Watan Disamban 2019, Kakakin ‘Yan Sandan jihar Imo, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa zargin zambar Naira miliyan 11 ce ta sa aka kama wannan babban Mawakin.

“Mun samu kara daga wani Mawaki wanda ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Imo a karkashin Owelle Rochas Okorocha ta ofishin Mai bada shawara kan harkokin nishadi, ta shiga wata yarjejeniya da Duncan Mighty domin ya shirya mata wakoki tare da wasu Mawaka da sunan kamfaninsa. A dalilin wannan aka ba shi Naira miliyan 11, har yau kuma bai cika alkawari ba.”

KU KARANTA: 'Yan ta'adda sun sake hallaka wasu Bayin Allah a Najeriya

“A dalilin wannan korafi, aka kama Mawakin, kuma ya tabbatar cewa an yi wannan yarjejeniya da shi, kuma ya karbi miliyoyin, amma ya ce abin da kurum zai sa ya maida kudin shi ne idan an soke kwangilar. A karshe aka bada belinsa bisa kimarsa.” Inji Kakakin ‘Yan Sandan jihar.

“Daga baya tsohon gwamnan Imo ya gabatar da takardar soke yarjejeniyar wannan kwangila domin Mawakin ya dawo da kudin da aka ba shi. Daga nan ya tsere, aka gaza gane inda ya shige.

Orlando Ikeokwu ya fitar da jawabi cewa a dalilin haka ne aka bada umarni a cafke Duncan Mighty, kuma aka kama shi a safiyar Ranar Asabar. Yanzu haka an bada belinsa ya koma gida.

Mai magana da yawun jami’an tsaron, DSP Ikeokwu, ya tabbatar da cewa sun saki shawararren Mawakin tare da karbar jingina. A mako mai zuwa zai kai kansa gaban ofishin ‘Yan Sanda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel