Ran matar aure ya baci ta bada lambar wayarta ga duk mai son lalata da ita, bayan ta kama mijinta yana iskanci da wata

Ran matar aure ya baci ta bada lambar wayarta ga duk mai son lalata da ita, bayan ta kama mijinta yana iskanci da wata

- Marubuci kuma mai bayar da shawara a kan zamantakewa, Joro Olumofin ya wallafa wani rubutun da ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta

- Wata matar aure ce ta turo mishi lambar wayarta a kan ya tuntubeta don kwanciya dashi, ta gaji da mugun halin mijinta na neman mata

- Matar ta bayyana yadda ta ga sakon kar ta kwana a wayar mijinta daga budurwarshi, tana tambayarshi ko ya kawo a ciki waccan saduwar tasu

Marubuci kuma mai bada shawara a kan zamantakewa Joro Olumofin ya girgiza da kalaman wata matar aure.

Matar mai zama a Abuja, ta fusata da halin maigidanta ne. Kamar yadda ta fadi, maigidan nata manemin mata ne kuma abun na kona mata rai.

Fusata da al'amarin neman matanshi ne yasa ta tura wa Joro sako mai dauke da lambar wayarta. A gaggauce take bukatar shi don kwanciya dashi.

Ta bukaci kwanciya dashi a ranar, gobe kuma a cigaba da hakan har abada.

"Barka da war haka Joro. Na shiga wani mummunan hali da tashin hankali. Na gaji da wannan mutumin da nake zaune dashi. Ka duba fa! Kawai na dauka wayarshi sai naci karo da sakon wata budurwarshi tana tambayarshi ko waccan kwanciyar da suka yi ko ya kawo a cikin jikinta."

"A yau zan kwanta da kai Joro, ga lambar wayata kaima ka turo min taka. Zan kwanta da kai yau, gobe kuma har abada zan cigaba. Na gaji da wannan bakin cikin." Matar tace.

KU KARANTA: Bincike: Kashi 63 na daliban jami'a ana lalata da su saboda shigar banzar da suke yi

Wannan lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani. Mutane da yawa sun ga gaskiyar matar tare da Alla-wadai da mummunan halin maigidanta. Sun kara da bata hakuri don tausasa mata zuciya.

A wani bangare kuwa, wasu sun fusata da matar inda suka shawarce ta da ba zuciyarta hakuri. Don kwanciya da wasu mazan da ba nata ba zai jawo mata karin matsala ne fiye da wacce take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel