Har ila yau: Jerin wasu kadarorin tsohon gwamna Kalu da EFCC zata kwace bayan an tura shi kurkuku

Har ila yau: Jerin wasu kadarorin tsohon gwamna Kalu da EFCC zata kwace bayan an tura shi kurkuku

A ranar Asabar ne hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta zakulo tare da tarkata kadarori mallakin Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattijai kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, don kwace wa.

An kama Kalu ne da laifuka 39 da suka hada da waskar da makudan kudade har N7.65bn daga baitul malin jihar Abia a lokacin da yake gwamna.

Kamar yadda EFCC ta ce, ta tarkata kadarorin ne don gudun kada su batan dabo bayan hukuncin daure shi a gidan gyaran hali da kotu ta yi masa.

A ranar 5 ga watan Disamba ne Jastis Muhammad Idris na babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihad Legas ya ce a tattara kamfanin Kalu mai suna Slok Nigeria Limited da wasu kadarorinsa don mikasu ga gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Aiyukan alherin marigayi Sani Abacha da kwata - kwata ba a maganarsu

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Kalu bai kara damuwa da halin da yake ciki ba, har sai lokacin da abokansa suka fara kai masa ziyara a gidan gyaran halin.

Bayan kotu ta yanke masa hukunci, Kalu ya tambayi jami’an gidan gyaran hali “Ina zamu je yanzu daga nan?” yayin da suke fitowa da shi daga harabar kotun.

Bayan kwanaki kalilan da yanke wa tsohon gwamnan hukuncin, wani abokinsa na kasuwanci ya kai, masa ziyara, har ya nuna ya girgiza da halin da ya ga tsohon gwamnan a ciki. Kalu na sanye da silifas a kafarsa yayin da abokin ya ziyarce shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel