Jiragen ruwa 27 dauke da man fetur da kayayyaki sun dira Najeriya

Jiragen ruwa 27 dauke da man fetur da kayayyaki sun dira Najeriya

Hukumar tashar ruwan Najeriya NPA ta ce jiragen ruwa 27 jibge da man fetur, kayyakin abinci da sauransu sun isa tashar jirgin ruwa Tin Can an shirin saukesu.

NPA ta bayyana hakan ne a mujallarta na 'Shipping Position' da kamfanin dillancin labaran anjeriya NAN ta samu ranar Juma'a.

Bisa ga rahoton, jiragen suna dauke kwantenonin gishiri, motoci, sikari, da man fetur.

Mujallarsa ta bayyana cewa jirage 30 aka sa ran zasu dira.

A wani labarin daban, Hadiza Bala Usman, manajan daraktan hukumar jiragen ruwa ta Najeriya, ta yi kira da cewa a binciki wasu mutane da take zargi da hantararta a farfajiyar majalisar dattijai.

A koken da ta mika ga sifeta janar din 'yan sanda, shugaban majalisar dattijai da kuma shugaban hukumar jami'an tsaro na fararen kaya, Usman ta yi bayanin zuwan da ta yi majalisar don amsa gayyatar da aka yi mata a majalisar.

Ta bayyana cewa, wasu mutane sun hareta wadanda take zargin hayarsu aka yi. Ta zargi Idahosa Okunbo, shugaban OMSL da wannan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel