Wasu gwamnoni na shirya tuggun maye Oshiomole da Yari

Wasu gwamnoni na shirya tuggun maye Oshiomole da Yari

Tsohon dan takaran gwamnan Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa wasu gwamnoni na kokarin tsige shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Adams Oshiomole domin daura tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari.

Yayinda yake magana da manema labarai a jihar Zamfara, Marafa yace gwamnonin na shirya hakan ne don kwace jam'iyyar domin siyasar 2023.

Sanatan wanda yaki bayyana sunayen gwamnonin, ya ce masu adawar shugaban jam'iyya, Adams Oshiomole, na harin shugaba Muhammadu Buhari domin rage masa karfin gwiwa wajen zaben wanda zai gajesa.

Yace: "Wannan ba yakin Oshiomole bane, aihinin wanda suke hara shugaba Buhari ne. Yanzu kawai ba suyi karfi bane amma idan ta nuna zasu fito fili."

"Ya bayyana karara cewa shirya tuggun tsige Kwamred Adams Oshiomole da wasu na kusa da shugaba Buhari keyi ya karfafa. Kawai suna kokarin kwace jam'iyyar ne su mikawa Yari - wanda har yanzu yana jin haushin shugaban kasa."

"Gwamnonin da abokansu, ciki da wajen jam'iyyar, suna iyakan kokarinsu wajen kwace jam'iyyar domin tabbatar da cewa shugaba Buhari da masoyansa basu da tacewa kan siyasar 2023."

Marafa ya yi kira ga shugaba Buhari yayi hattara da Yari inda ya bayyana wurare daban-daban da yaudari Buhari.

A bangare guda, Sanata Kabiru Marafa, ya nisanta kansa daga rahoton cewa an yi zaman sulhu tsakanin yan bangarensa da tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari.

Za ku tuna cewa kakakin bangaren Yari na jam'iyyar APC a jihar, Shehu Isah, ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya gana da wasu mambobin bangaren Kabiru Marafa domin dinke barakar da ke tsakaninsu.

Wannan rikici ya sabbabawa jam'iyyar biyu babu a zaben bara inda kotu ta mikawa jam'iyyar PDP mulki bulus.

A martani Marafa kan rahoton, ya ce bashi da masaniya game da zaman sulhun da ake radawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel