Fani-Kayode ya yi magana kan komawarsa APC

Fani-Kayode ya yi magana kan komawarsa APC

Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Femi Fani-Kayode ya ce ya gwammace ya mutu da ya shiga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki yanzu a kasar.

Ya yi wannan furucin ne yayin mayar da martani kan jita-jita da aka yi na cewa ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC).

Tsohon ministan ya ce cin fuska ne a danganta shi da abind ya kira 'jirgi mai nutsewa mai dauda kamar APC."

A wani jawabin da ya wallafa a shafinsa na Twitter @realFFK, ya rubuta, "Batun cewa na fice daga @OfficialPDPNig na koma @OfficialAPCNg cin mutunci ne a gare ni kuma tsantsagwaron karya ne."

DUBA WANNAN: Tirkashi: Matashi mai shekaru 19 dirka wa mahaifiyarsa cikin shege

"Ya kamata wadanda ke yada wannan labaran karyan su ji kunya.

"Na gwammace in mutu da in shiga dadaudar jirgin da bereye suka lalata ta da kuma ke nutsewa kamar jam'iyyar APC."

Fano-Kayode ya dade yana sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A halin yanzu gwamnati mai ci yanzu na bincikarsa kan zargin aikata rashawa.

Ga sakon da ya wallafa a Twitter a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel