Yan ta'addan ISWAP sun hallaka ma'aikatan kungiyar jinkai AAH guda 4

Yan ta'addan ISWAP sun hallaka ma'aikatan kungiyar jinkai AAH guda 4

Kungiyar daular addinin Musulunci a yankin Afrika ta yamma ISWAP sun hallaka ma'aikatan kungiyar jinkai da tallafin Action Against Hunger da suka sace tun watar Yulin 2019.

Yan ta'addan ISWAP sun yi garkuwa da jami'an tallafin ne guda shida a ranar 19 ga watan Yulin shekarar nan.

Shahrarren dan jaridan da ya shahara da kawo rahoto kan Boko Haram, Ahmad Salkida, ya bayyana labarin a ranar Juma'a.

Ya ce cikin mutane shidan da suka sace, basu kashe mace daya dake cikinsu ba, Grace Taku, amma sun mayar da ita baiwa har abada.

Salkida yace: "ISWAP sun sake kashe mutane hudu, sun saki bidiyon. Dukkan jami'an tallafin hudu yan kungiyar yaki da yunwa Action Against Hunger ne da aka sace tun watan Yulin, 2019. Mace dayan dake cikinsu, Garce Taku, ta zama baiwa."

Salkida ya ce yan ta'addan sun hallaka mutanen ne saboda rashin cika alkawari na gwamnatin tarayya.

Yace: "ISWAP ta yi ikirarin cewa sun kashesu ne sakamakon rashin cimma matsaya a tattaunawarsu da gwamnati."

"Gwamnatin ba ta gaskiya, ba ta cika alkawari," ya ruwaito daga majiya

Zaku tuna cewa a ranar 19 ga Yuni, 2019, yan ta'addan ISWAP sun kashe direba sannan suka sace ma'aikatan kungiyar AAH a Damasak, jihar Borno.

Hakan ya biyo bayan kisan Saifur Ahmed, ma'aikaciyar UNICEF da Hauwa Liman da Boko Haram sukayi a watan Oktoban, 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel