Muna goyon bayan kafa sabbin masarautu - Kungiyar dattawa Kano

Muna goyon bayan kafa sabbin masarautu - Kungiyar dattawa Kano

Wasu yan kungiyar dattawan jihar Kano mai suna Kano Integrity Forum, sun bayyana cewa kafa sabbin masarautu a rahamace ga jihar Kano.

A wata hira da manema labarai, shugaban kungiyar, Farfesa Abdu Salihi, ya ce kafa sabbin masarautu zai samar da aikin yi ga matasan da ke zaman banza.

Farfesa Salihi, wanda tsohon kwamishanan noma ne a jihar, ya ce kauyuka da yawa karkashin sabbin masarautun hudu zasu zama birane ta hanyar samun ayyukan jin dadin al'umma irinsu asibitoci da makarantun gaba da sakandare.

Hakazalika ya ce sabbin masarautun za ta taimaka wajen dakile matsalolin tsaro a jihar ta hanyar kusantar da mutane ga gwamnati.

Yace:"Kafa sabbin masarautu a jihar ya jawo cece-kuce cikin al'umma, a matsayinmu na kungiyar Kano Integrity Forum, bisa ga tarihinmu, muna maraba da wannan mataki."

"Mun yanke shawaran hakan ne gan bayanan da muka gani a kasa musamman na shirye-shiryen cigaban al'umma."

Farfesa Salihi ya kara da cewa wadanda ke nuna adawa da kafa sabbin masarautun da hujjan cewa ya saba tarihi, sun manta cewa babu tarihin da ba'a iya canzawa.

KARANTA NAN Yan ta'addan ISWAP sun hallaka ma'aikatan kungiyar jinkai AAH guda 4

A bangare guda, Gwamnatin jihar Kano tace hukuncin babbar kotun jihar kan sabuwar majalisar sarakuna bai da alaka da kafa sabbin masarautu hudu da gwamnan yayi.

Jawabin da ministan yada labaran jihar, Malam Muhammad Garba, ya saki ya bayyana cewa wasu masu adawa da sabbin masarautun ne ke yada jita-jitan cewa kotu ta soke masarautu.

Jawabin ya kara da cewa yan adawan za su sha mamaki idan kotu ta yanke hukunci kan lamarin sabbin masarautun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel