Gwamnonin PDP biyu sun yi cacar baki a kan Buhari

Gwamnonin PDP biyu sun yi cacar baki a kan Buhari

- An ruwaito yadda wasu gwamnoni biyu na jam’iyyar PDP suka yi cacar baki a kan Buhari

- Gwamna Wike na jihar Ribas ya kira Gwamna Umahi na jihar Ebonyi da ‘mutumin Buhari’

- A mayar da martani da Umahi ya yi, ya yi barazanar sakin hotunan Wike tare da Buhari

An yi karamin wasan kwaikwayo tsakanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da kuma gwamnan jihar Ebonyi, a kan tsokaci kan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar The Nation ta ruwaito yadda ‘wasan kwaikwayon’ ya fara sa'adda Gwamna Wike ya yi wa Gwamna Umahi ba’a a kan dangantakarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng ta gano cewa, Gwamna Umahi ne gwamnan jam’iyyar PDP mafi kusanci da Shugaban kasa Buhari. Hakazalika, gwamnan ba ya boye komai na kusancinsa da Shugaban kasar. Hakan kuwa ya jawo jita-jita da aka dinga yadawa a baya, na cewa gwamnan zai canza sheka zuwa jam’iyyar APC.

DUBA WANNAN: Rikicin fadar shugaban kasa: 'Yan garinsu Buhari sun yi wa Aisha kaca-kaca

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Wike ya yi ba’a a kan dangantakar da ke tsakanin Buhari da Umahi a yayin wani taronsu. Hakan kuwa ya harzuka gwamnan jihar Ebonyi din, dalilin da yasa suka kusa ‘ba hammata iska’.

Tun farkon isowar Gwamna Umahi, Wike ya fara yi masa ba’a inda ya ce, “Ahh, mutumin Buhari ya iso!”.

Wannan kalamai kuwa sun sa sauran gwamnonin bushewa da dariya, amma hakan bai yi wa Umahi dadi ba don a take ya mayar da martani.

Ya ce: “Wane ne yafi shigewa Buhari fiye da kai? Ina da hotunanku da yawa tare da Buhari wadanda mutane basu sani ba.”

A nan take kuma Umahi ya yi barazanar sakin hotunan matukar Wike ya cigaba da harzuka shi.

“Toh fah, Wadanda ke wajen sun sanar da cewa Wike ya yi mukus. Martanin Umahi kuwa ya kashe bakin Wike a kan tattauna zancen Buhari kuma an cigaba da taron lafiya,” kamar yadda majiyar ta sanar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel