Yanzu-yanzu: Mahaifiyar Mimiko ta rasu

Yanzu-yanzu: Mahaifiyar Mimiko ta rasu

Misis Muyinat Mimiko, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Ondo, Dakta Olusegun Mimiko ta rasu.

The Punch ta ruwaito cewa ta rasu ne bayan fama da gajeruwan rashin lafiya a gidan ta da ke Ondo.

Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 88 a duniya.

Wani hadimin tsohon gwamnan, Mista Paul Akinduro, wanda ya tabbatar wa majiyar Legit.ng rasuwar a ranar Asabar ya ce dattijuwar ta rasu ne a daren Juma'a.

DUBA WANNAN: Allah bashi da ɗa: Wata mata ta fizge amsa kuwwa daga hannun fasto yayin wa'azi a kasuwa

Ya ce, "Mama Muniyat Mosekola Mimiko da ake saba kira da 'Iye Ruka' ta riga mu gidan gaskiya. Za muyi kewan ta sosai."

Ku cigaba da kasancewa da mu don samun cikakken rahoton...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel