Kungyoyin daliban BUK sun ki amince da karin kudin makaranta, sun bayar da sharadi

Kungyoyin daliban BUK sun ki amince da karin kudin makaranta, sun bayar da sharadi

Kungiyar daliban jami'ar BUK ta yi watsi da karin kudin makaranta da hukumar jami'ar ta yi. Karin ya hada da kudin dakunan kwanan dalibai da na makaranta. Hukumar makarantar ta sanar da hakan ne a takardar da ta fitar a ranar Juma'a, 6 ga watan Disamba 2019.

Hakan na daga cikin hukuncin da kungiyar wakilan dalibai, kungiyar dalibai musulmai da sauran kungiyoyin dalibai suka yanke a taron da suka yi a ranar Asabar.

Idan zamu tuna, an gano cewa hukumar zartarwa ta jami'ar ta amince da karin kudin makaranta a taronta kashi na 378. Hakan ya bayyana ne a mujallar da jami'ar ta fitar.

Kamar yadda mujallar ta fitar, an samu karin kudin dakunan kwanan dalibai.

DUBA WANNAN: Rikicin fadar shugaban kasa: 'Yan garinsu Buhari sun yi wa Aisha kaca-kaca

Dakin dalibai masu digiri na farko ya tashi daga N12,090 zuwa N20,090. Sai kuma gado babu katifa ya tashi daga N7,090 zuwa N12,090.

A wata wasika da aka rubuta zuwa shugaban jami'ar wacce Shugaban daliban makarantar Sadi Garba, Shugaban dalibai musulmai Lukman Usman Aliyu da Shugaban Aso BUK Fakhrudeen Auwal Taheer suka sa hannu, sun bayyana mamakinsu a kan yadda aka yi karin ba tare da an tuntubesu ba.

Wasikar ta bukaci bayanin a kan kare-karen da aka yi wa dalibai a kudin makaranta.

Kungiyoyin sun ba da wa'adin zuwa ranar Juma'a ga hukumar jami'ar da su yi bayanin da ya dace a kan karin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel