Abubuwa 7 da suka faru a shekarar 2019 wadanda suka kawo kace-nace a Najeriya

Abubuwa 7 da suka faru a shekarar 2019 wadanda suka kawo kace-nace a Najeriya

- Shekarar 2019 na bankwana amma akwai abubuwa masu yawa da za a ringa tunawa

- Al'amuran da suka faru na da yawa, ballantana wadanda suka shafi sanannun mutane

- Ga wasu maudu'ai da suka jawo cece-kuce a kafofin sada zumuntar zamani

A yayin da shekarar 2019 ke zuwa karshe, zamu iya cewa 'yan Najeriya a wannan shekarar sun samu maudu'ai kala-kala kamar kowacce shekara. Zamu iya cewa, ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ne suka fi samun abubuwan tattaunawan. Wasu abubuwan bakin ciki, wasu na farin ciki amma wasu na ban dariya ne. Inda aka fi baje kolin dai ita ce Tuwita. Legit.ng ta tattaro muku maudu'ai biyar masu zafi da aka dinga tattaunawa.

1. Fatoyinbo da Busola Dakolo.

A wannan shekarar, matar sanannen mawaki Timi Dakolo Busola ta zargi babban fasto Biodun Fatoyinbo da cin zarafinta lokacin tana karama. Wannan zargin ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya. Wasu na kira da a yi mata adalci amma wasu basu yarda da zargin ba.

2. Elisha Abbo

Wani bidiyon Sanata Elisha Abbo ya bazu inda yake dukan wata matashiyar budurwa a wani shago. Mutane da yawa sun bukaci a yi wa budurwar adalci. Amma daga baya, sanatan ya fito ya bada hakurin abinda yayi.

3. Regina Daniels da Ned Nwoko

Auren Regina Daniels da tsohon dan siyasa, Ned Nwoko ya sha maganganu kala-kala a kafafen sada zumuntar zamani. Duk da hakan, masoyanta sunyi mata Alla-sam barka.

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutumi ya gama shiri tsaf domin auren wata mutum-mutumi da ya siya don ya dinga jima'i da ita maimakon mace 'yar adam

4. Zanga-zangar sakin Naira Marley

EFCC ta cafke Naira Marley a kan zarginshi da take yi da damfara. Kafin a sako shi, magoya bayanshi sun cika kafafen sada zumuntar zamani da yekuwar a sako Naira Marley. Ba nan ba kadai, har kan tituna sunyi zanga-zangar.

5. Big Brother Naija

Wannan shiri ne da ke nishadantar da 'yan Najeriya kuma shiyasa suke maganarshi a koda yaushe. Ya faru a wannan shekarar.

6. Auren Glory Osei

Wannan mace ce mai rajin kare hakkin mata. An zargeta da boye labarin aurenta amma tana fitowa a shafinta na tuwita don batar da mata. Duk da ta fito ta yi bayani dalla-dalla, maudu'inta ya yi tashe na kwanaki.

7. Yayin Otedola

'Yan Najeriya sunyi caa a kan biloniya Otedola bayan da ya garzaya har kasar Italiya don siyan askirim.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel