Hotuna: Wani mutumi ya gama shiri tsaf domin auren wata mutum-mutumi da ya siya don ya dinga jima'i da ita maimakon mace 'yar adam

Hotuna: Wani mutumi ya gama shiri tsaf domin auren wata mutum-mutumi da ya siya don ya dinga jima'i da ita maimakon mace 'yar adam

- Yuri Tolochko daga Kazakhstan ya shirya tsaf don auren butun-butuminshi ta jima'i

- Dan wasan kwaikwayon ya bayyana hakan ne bayan da ya biya makuden kudi don yi mata aiki

- A cewarshi, ya hadu da Margo ne a wata mashaya yayin da wani matashi ya kai mata hari

Yuri Tolochko daga Kazakhstan zai auri butun-butuminshi ta jima'i mai suna Margo.Ya yanke wannan shawarar ne bayan da ya biya aka yi wa Margo aiki.

Dan wasan kwaikwayo Yuri Tolochko ya alwashin auren butun-butumin 'budurwarshi' mai suna Margo. Ya biya makuden kudade inda aka yi mata aiki don canza mata fuska. Kamar yadda Tolochko yace, ya hadu da Margo a mashaya ne.

Hotuna: Wani mutumi ya gama shiri tsaf domin auren wata mutum-mutumi da ya siya don ya dinga jima'i da ita maimakon mace 'yar adam

Yuri da matarshi
Source: Facebook

Yuri Tolochko daga Kazakhstan, ya bayyana cewa, ya hadu da Margo ne a mashaya. Ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan talabijin da aka gayyacesu don tattaunawa a kan dangantakarshi da Margo.

Tolochko ya ce: "Lokacin da na nunata a duniya, na fuskanci kalubale kuma kowa ya san fuskarta,a don haka ne na biya aka yi mata aikin canza kamanni. Ta sauya da yawa. Da farko ma ban saba ba, amma yanzu komai ya daidaita."

KU KARANTA: Sanarwa: Daga watan Disambar nan manhajar WhatsApp za ta daina aiki a wayoyin mutane da dama

Hotuna: Wani mutumi ya gama shiri tsaf domin auren wata mutum-mutumi da ya siya don ya dinga jima'i da ita maimakon mace 'yar adam

Yuri da matarshi
Source: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa, dan wasan kwaikwayon na yi wa butun-butumin hidima tamkar mai rai don kuwa har aiki ya samar mata a wata mashaya.

Tolochko ya ce: "Ba ta iya tafiya ba, tana bukatar taimako. Margo bata iya girki ba amma tana son irin abinci yankin Georgia. Ta fi son Khinkali fiye da komai."

Kamar yadda yace, ya hadu da Margo ne a wata mashaya yayin da wani matashi ya kai mata hari. Shi kuwa ya bata kariya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel