Gwamnatin Ghana ta hana hukumomin kasar sayan shinkafar kasashen waje

Gwamnatin Ghana ta hana hukumomin kasar sayan shinkafar kasashen waje

Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana ya umurci hukumomin kasar su fara sayan shinkafar da ake nomawa a kasar daga watan Janairun 2020.

The Cable ta ruwaito cewa ya bayar da umurnin ne yayin zantawa da manena labarai a gidan Jubilee a Accra a ranar Juma'a.

Akufo-Addo ya ce an dauki matakin ne domin tallafawa manoman kasar su inganta noman shinkafa.

Ya ce shinkafar da aka noma a kasar ake ci a gidansa, ya kara da cewa dole hukumomin kasar su tallafawa kasar a yunkurin ta na tabbatar da cewa ta dogara da kanta.

DUBA WANNAN: Allah bashi da ɗa: Wata mata ta fizge amsa kuwwa daga hannun fasto yayin wa'azi a kasuwa

Ya ce, "Dukkan mu zamu bayar da gudunmawa wurin ganin mun dogara da kan mu, ya kamata dukkanmu mu rika cin shinkafar Ghana. Mu fadawa matan mu da 'yan uwan mu da duk wanda ke siyo abinci a gida ya rika siyo shinkafan Ghana."

Shugaban kasar ya ce gwamnatnsa na kokarin tallafawa manoman shinkafa na kasar ta hanyar gina manyan rumbunan ajiyar kayan abinci da kuma kafa hukumar musayar kayayyaki na Ghana.

A yayin bikin ranar manoma da aka yi a kasar makon da ya gabata, Akufo-Addo ya yi kira ga al'ummar kasar su rika cin shinkafar da ake nomawa a kasar.

Ya ce, "Shirin gwamnati na tabbatar da kasar da dogara da kanta zai yi nasara ne idan mutane sun fara cin shinkafar da ake nomawa a kasar don tallafawa manoma."

"Ya zama dole mu rika cin abinda muke nomawa don tallafawa manoman mu, su taimakawa masu noma abinci a kasarmu. Mata ta Rebecca da dage dole sai mun rika cin shinkafar Ghana a gidan mu. Ina kira da dukkan yan Ghana su yi koyi da mu."

Mutane sun fara cin shinkafar da ake nomawa a gida Najeriya tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin rufe iyakokin kasar na kasa.

Shugaba Buhari ya bayar da umurnin rufe iyakokin kasar ne don rage fasakwabri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel