Tsohon gwamna Kalu ya yi magana daga gidan yari, ya fadi irin abincin da ake bashi

Tsohon gwamna Kalu ya yi magana daga gidan yari, ya fadi irin abincin da ake bashi

-Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya yi magana a kan halin da yake ciki a gidan gyaran hali

- Babbar kotun tarayya dake Legas ce ta yanke wa tsohon gwamnan hukunci a cikin watan Disamba, 2019

- A wani rahoto da jaridar The Nation ta wallafa, Kalu ya sanar da yadda ake ciyar da shi a gidan

Jaridar The Nation ta ruwaito yadda tsohon gwamnan jihar Abia kuma Sanata a halin yanzu, Orji Uzor Kalu, ya bayyana yadda ake ciyar da shi a gidan gyaran halin.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda aka yanke wa bulaliyar majalisar datiijan hukuncin shekaru 12 a gidan gyaran hali. Babbar kotun tarayya da ke Legas ce ta yanke hukuncin bayan da ta kama shi dumu-dumu da laifin damfarar N7.65bn a yayin da yake gwamnan jihar Abia.

Idan zamu tuna, Kalu ya zama gwamnan jihar Abia a lokacin da bai kai shekaru 40 ba a duniya kuma ya mulki jihar ne na tsawon shekaru takwas.

DUBA WANNAN: Asirin wani dan yankan kai da ke haukar karya ta tonu (Hoto)

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Kalu bai kara damuwa da halin da yake ciki ba, har sai lokacin da abokansa suka fara kai masa ziyara a gidan gyaran halin.

Bayan kotu ta yanke masa hukunci, Kalu ya tambayi jami’an gidan gyaran hali “Ina zamu je yanzu daga nan?” yayin da suke fitowa da shi daga harabar kotun.

Bayan kwanaki kalilan da yanke wa tsohon gwamnan hukuncin, wani abokinsa na kasuwanci ya kai, masa ziyara, har ya nuna ya girgiza da halin da ya ga tsohon gwamnan a ciki. Kalu na sanye da silifas a kafarsa yayin da abokin ya ziyarce shi.

“Kalli yadda nake cin abinci a gidan yari,” ladabtaccen gwamnan ya sanar da bakonsa yayin da yake neman kalaman kwantar da hankali da zai furta masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel